✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kebbi ta kashe Naira miliyan 99 wajen biyan hakkokin tsofaffin shugabannin kananan hukumomi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kashe sama da Naira miliyan 99 domin biyan tsofaffin shugabannin kananan hukumomin jihar 21 hakkokinsu. Babban Sakataren Ma’aikatar kananan…

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta kashe sama da Naira miliyan 99 domin biyan tsofaffin shugabannin kananan hukumomin jihar 21 hakkokinsu.

Babban Sakataren Ma’aikatar kananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu ta Jihar, Malam Sani Muhammed Yeldu, ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa, inda ya ce tsofaffin shugabannin da aka biya sun haxa da waxanda suka yi mulki daga shekarar 2004 zuwa 2008, waxanda suka samu kashi 30 cikin 100, wadanda suka shugabanci kananan hukumomi daga shekarar 2014 zuwa 2015 suka samu kashi 40 cikin 100.

Babban Sakataren ya ce tsofaffin shugabannin yankunan na riko na shekarar 2014 zuwa 2015 a lokacin tsohon Gwamna Sa’idu Xakingari sun samu nasu kaso a cikin wannan biyan.

Malam Sani Yeldu ya ce baya ga wannan, gwamnatin jihar ta sake bayar da Naira miliyan 100, domin tallafa wa malamman makarantun firamare 1,767 da makarantun Islamiyya da ma’aikatan asibitocin karkara, inda ya ce wannan bangaren za a kaddamar da shi nan ba da jimawa ba.

A zantawarsa da Aminiya, Shugaban kungiyar Tsofaffin Kansiloli ta Jihar Kebbi, Alhaji Usman Ibrahim Maiyaki, ya gode wa gwamnatin jihar, kan wannan kokari da ta yi, kuma ya ce an kafa kwamiti na musamman domin ganin cewa duk wanda ke da haki an biya shi yadda ya kamata.

 Game da shugabannin da suka rasu, ya ce, kwamitin zai zagaya domin tuntubar iyalansu don ganin an mika musu hakkinsu.