An ɗaura haramar gabatar da ƙudirin ƙirƙiro sabuwar Jihar Tiga da za a fitar daga Jihar Kano.
Wakilin Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Sanata Kawu Sumaila ne ya miƙa ƙudirin da ke neman yi wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya kwaskwarima na ƙirƙiro jihar ta Tiga.
- Ganduje da matarsa za su bayyana a kotu kan zargin almundahana
- Buni ya dakatar da shugaban ƙaramar hukuma kan rashin ɗa’a
An dai sanya yi wa ƙudirin karatun farko a cikin jerin mas’alolin da Majalisar Dattawan za ta yi bita a kai yayin zamanta na wannan Larabar.
Sai dai buƙatar hakan ba ta yiwu ba sakamakon ɗage zaman majalisar da aka yi zuwa gobe Alhamis a dalilin rasuwar wani ɗan Majalisar Wakilai, Honarabul Olaide Adewale Akinremi.
A halin yanzu dai Jihar Kano tana ƙunshe da ƙananan hukumomi 44 kuma ɗaya daga cikin jihohin mafi yawan jama’a a ƙasar.
Haka kuma, Jihar Kano wadda ke Arewa maso Yamma tana yankin da ya fi kowanne yawan jihohi a ƙasar.
A yayin da kowanne ɗaya daga cikin yankunan Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma ke da jihohi shida-shida, yankin Arewa maso Yamma na ɗauke da jihohi bakwai.
Aminiya ta ruwaito cewa, a baya bayan nan aka soma kiraye-kirayen ƙirƙirar wata sabuwar jiha a Kudu maso Gabashin Nijeriya. Majalisar Wakilai ta gabatar da ƙudurin ƙirƙiro ƙarin jiha guda da za a kira Jihar Etiti a yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Honarabul Amobi Godwin Ogah tare da wasu ’yan majalisa huɗu ne suka gabatar da ƙudirin a farko wannan watan na Yuli.
Ƙudurin na buƙatar yin gyara a sashe na uku na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar, domin goge lamba 36 tare da maye gurbinta da lamba 37 don bai wa sabuwar jihar damar shiga jerin jihohin ƙasar, sannan a saka Etiti bayan Enugu cikin jerin sunayen jihohin ƙasar.
Sabuwar jihar wadda za a yanka daga duka jihohin yankin biyar za ta ƙunshi ƙananan hukumomi 11, inda Lokpanta da a yanzu ke cikin Jihar Abia, zai kasance babban birninta.
Ƙananan hukumomin da za su koma sabuwar jihar sun haɗa da Isuikwuato da Umu-Nneochi (Jihar Abia), da Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu (Jihar Anambra), sannan Ivo da Ohaozara (Jihar Ebonyi), sai Aninri da Agwu da Oji River (Jihar Enugu), da kuma Okigwe da Onuimo (Jihar Imo).