✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

KAWALWALNIYA

Sharhi: Wakar kawalwalniya an rubuta ta ne da nufin fadakarwa da tsoratarwa game da lamarin duniya. Ma’anar takenta ya samu ne ta kamanceceniya da kawalwalniya,…

Sharhi: Wakar kawalwalniya an rubuta ta ne da nufin fadakarwa da tsoratarwa game da lamarin duniya. Ma’anar takenta ya samu ne ta kamanceceniya da kawalwalniya, wato “ruwan fako” – ruwan gangan, wanda matafiyi ke hangowa daga nesa kamar ruwa, alhali babu komai.

Babi 11 ne ga wakar, ’yar kwar biyu, wacce ke karewa da kafiyar “ba.”

A baiti na farko, an bayyana duniya da cewa gida ne na jarabawa, inda ake hakilo tsakanin karya da gaskiya, tsakanin samu da rashi, tsakanin yunwa da koshi, tsakanin karfi da rauni. A baiti na biyu, ana jan hankalin mutane da su lura da cewa duniya gudu gare ta, lokaci ba ya jiran kowa. Ke nan ya dace mutum ya yi amfani da lokacinsa wajen aikata abin alheri. A baiti na uku, an fasalta duniya da hargitsattsa, wacce ke bijiro da abubuwa ba kai ba gindi. Ke nan ana nufin ya kamata mutum ya natsu, duk abin da zai aikata a rayuwarsa, ya tsara shi yadda ya dace. Mutum ya kasance mai bin komai bisa tsari, ya rika yin komai daidai iyawarsa, daidai ruwa-daidai kurji.

A baiti na hudu, shi ma gargadi ne ga mutane, cewa su daina shagala, su ci gajiyar ayyukan kirki. Idan mutum ya shagala da duniya, kamar yadda baitin ke nunawa, to zai iya asara babba a rayuwarsa. Idan ciwon kaba ya kama mutum, ai kuwa ya bani. Baituka na biyar da na shida kuwa suna kara tsoratar da mutane ne game da duniya, cewa gida ne na fitina da jidali, babu babba ba yaro, ba mace ba namiji.

Baituka na bakwai da na takwas kuwa, duk dai tsoratarwa suke yi, cewa babu hutu a duniya, idan ma har tana da romo, to romon naman karya ne, mai wari. Haka ma baiti na tara da na goma da na sha daya, suna nuna yadda duniya ta kasance mai ido tsakar ka, wacce ba ta la’akarin wanda za ta dauka kuma ba ta tarar wanda za ta jefar. Don haka duk wanda ya auri duniya, to tamkar ya daura aure da karuwa ce, ba zai samu farin ciki ba.  

Duniya gidan jaraba,

Gidan fada sai dai a raba.

Duniya mai shara gudu,

Kan a ce ta kai Taraba.

Duniya ita ba ta shiri,

Kana gani sai tababa.

Duniya gidan shagala,

In kai sake ka sam kaba.

Duniya gidan fitina,

Ga wasu na cikin takaba.

Duniya gidan jidali,

Babu inna ba baba.

Duniya mai ‘yar shigifa,

Inuwarta ba hutu ba.

Duniya romon karya,

Mumini ba ya lasa ba.

Duniya ido a tsaka,

Zabenta ba haiba.

Duniya ita karuwa ce,

Aurenta to ina riba?

Duniya zaluma ce,

Kasgama uwar jaraba.