A koyaushe Ubangiji Allah Ya zabi Ya yi aiki da mutum ta wurin dangantakar da ke tsakanin Shi da mutum; Shi ne kuma ake ce da ita alkawari. A cikin Tsohon Alkawali dai, dukan mutanen da suka zama kayan aiki a hanun Ubangiji Allah, mutane ne da Allah Ya shiga yarjejeniya da su, mutane ne wadanda Allah Ya yi musu alkawari, ta wurin irin wannan alkawari ne Ubangiji Allah Yakan gwada Ya kuma duba wadanda suka iya rike nasu sashin alkawarin; domin a cikin kowace irin yarjejeniya; akwai sashi biyu – kowa da nasa bangaren. Allah zai rike naSa domin ba zai taba kasawa ba, idan mutum ya rike nasa sashin, to babu shakka Ubangiji Allah zai kaunace shi Ya kuma sa masa albarka mai yawa domin ya nuna kaunarsa ga Allah Madaukaki ta wurin yin biyayya ga maganarSa.
Haka nan a Sabon Alkawari, wannan yarjejeniyar an kafa ta a kan zubar da jinin Yesu Kiristi ne, bisa gicciye, a yau, dukan wadanda suka ba da gaskiya ga Yesu Kiristi, sun rigaya sun shiga cikin wannan alkawarin; idan kuwa mun ci gaba da yin biyayya; to gaskiyar ita ce, za mu ga albarkar Ubangiji Allah a kanmu a kullum. Akwai abubuwa kadan da a koyaushe ba su canjawa, suna nan kamar haka: Shirin yin albarkar nan na Allah ne. Wannan kuwa zai tabbata ne kawai ta wurin jinin alkawari da ya fanshi masu bin Yesu Kiristi kadai; Dukan wanda ya yarda ya shiga ciki kuwa, dole ne ya mika kansa ga yin biyayya da umarnin Ubangiji Allah, a karshe kuma Ubangiji ya yi alkawarin sa albarkarsa bisa mutanensa, wadannan sharudda ba su canja ba, kuma ba za su canja ba. Ko a Tsohon Alkawali ko kuma a Sabon Alkawali.
Wadannan albarkoki sun kunshi: Allah Mai aminci ne Shi: “Ka sani fa Ubangiji Allahnka, shi ne Allah; Allah Mai aminci, Mai kiyaye alkawari da jinkai ga masu kaunarsa da masu bin dokokinsa har zuwa tsara dubu.”(Kubawar Shari’a 7 : 9). Allah ba zai taba karya alkawarin da Ya yi ba, Shi Allah ba Ya canjawa, kamar yadda Yake a da haka Yake a yau, haka zai zama har abada, ba Ya canja magana. Komai Ya alkawarta kuma babu shakka zai aikata su. Za mu iya dogara ga maganarSa domin Shi Allah ba Ya karya, ba Ya yaudarar mutum, ashe za mu iya dogara ga kowane abin Ya yi alkawari cewa zai ba su. Allah Shi Mai aminci ne, Yana rike alkawarinSa ta kauna har zuwa ga tsara dubu. Albarkar da zai sako mutum wanda yake tsoronSa, ba shi kadai ne zai amfana da ita ba, amma har da ’ya’ya da jikokinsa da jikokin jikokinsa, haka zai ci gaba gaba har har har…… ashe tsoron Ubangiji Allah gado ne mai kyau wanda iyaye za su bar wa ’ya’yansu. Mu koya wa yaranmu jin tsoron Allah da kuma kaunar Allah, domin su yi rayuwar da za ta gamshi Allah. Shi Wanda muke bauta wa Mai aminci ne zai cika alkawarin na yi mana albarkar da Ya alkawarta.
Allah Mai nagarta ne: “Nagarta da jinkai kadai za su bi ni dukan kwanakin raina: Zan zauna kuma cikin gidan Ubangiji har abada.” (Zabura 23: 6). Wannan Allah Mai nagarta ne a koyaushe; duk wanda yake kaunarSa kuma zai yi tafiya ne cikin wannan alheri. Idan jinkan Allah na bin mutum a koyaushe, ba karamar albarka ba ce, abu guda da ya kamata mutum ya kudurta cikin zuciyarsa shi ne, mu zama masu son zama cikin Ubangiji Allah a koyaushe; haka ne za mu ga jinkanSa a kanmu dukan kwanakin ranmu.
Allah ne ke tsare mu: “Ubangiji Yana kiyaye dukan wadanda ke kaunarSa. Amma zai hallaka dukan miyagu.” (Zabura 145: 20). Babu wani abu da ya fi tsarewar da mutum zai samu daga wurin Allah. Babu wata dabarar mutum da take da iko ta tsare mutum daga kowane irin hadari idan ba daga wurin Ubangiji Allah ba. Muna cikin mawuyacin lokaci yanzu, mutane da yawa sun bar tsoron Allah sun koma ga tsafi da kuma gargajiya, a ganinsu gwamma sun je wajen bokaye da masu sihiri su yi musu wata dabara da za ta tsare su daga masifa da sauransu; amma babu wata dabara da mutum zai yi maka wanda take da iko ta tsare mutum daga kalubalen wannan zamani. Dukan wadanda suka gane cewa Allah Shi kadai ke da cikakken iko Ya tsare kowane mutum da yake kaunarSa. To ashe asirin na cikin nuna kaunarmu ne ga Allah ta wurin tafiya cikin nufinSa.
Samun Allah cikin dukan abu: “Ina kaunar wadanda ke kaunata, Wadanda ke bida ta da himma za su same ni.” (Misalai 8: 17). Wannan babbar albarka ce cewa mutum ya iya samun Allah. Allah Yana ko’ina, amma ba kowa ba ne kan iya samunSa, Allah Ya cika ko’ina amma ba lallai ba ne ka iya samunSa, shi Allah Yana lura da zuciyar mutum da kuma irin kwazo da sa kai cikin wurin nemanSa ba domin Allah Ya bata ba, amma domin Allah ba Ya bayyana kanSa ga mutumin da bai neme Shi da dukan zuciyarsa ba. Idan ka ce kana neman Ubangiji, to shi Allah zai soma duba yanayin zuciyarka da tunaninka; Ya gani ko da gaske ne kana bidarsa ko kuwa dai kawai kana yi ne domin kowa ma yana yi? Idan Ubangiji Allah Ya binciki cikin zuciyarka Ya kuma ga da gaske ne kana nemanSa, to zai bayyana kanSa gare ka. Idan kuwa cikin ibadarmu mun kai ga ganin yadda Allah Yake bayyana kanSa gare mu, to ba karamin abu ba ne ko kadan. Albarka ce da ta fi gaban kimantuwa. Bari ya zama cewa duk lokacin da muka dukufa ga neman fuskar Ubangiji Allah; ba zai samu wani abu kazantacce a cikinmu wanda zai hana Shi bayyana a gare mu ba.
Dukan abu suna aikatawa zuwa alheri: “Mun sani kuma dukan al’amura suna aikatawa zuwa alheri ga wadanda ke kaunar Allah, wato wadanda ke kirayayyu bisa kadararsu.” (Romawa 8: 28). Akwai lokatai da dama da abubuwan da ke faruwa da mutum a lokacin ba abubuwa ne masu faranta wa mutum zuciya ba, mai yiwuwa mummunan abu ne a ganin mutum; duk da haka, idan mutum yana gane cewa babu wani abu da zai faru da shi – ko mai kyau ko wanda bai da kyau bisa ga tunanin mutum wanda Allah bai sani ba. Allah Ya san komai duka, kuma Shi Allah ba Ya kuskure ko kadan. Dukan wadanda suke kaunarSa kuma sun san cewa duk abin da Allah Ya yi, suna aikatawa ne zuwa alheri. Wannan babbar albarka ce sosai.
Allah Yana zaune cikinsu: “Mun sani mun gaskanta kuma kauna wadda Allah Yake da ita a wurinmu. Allah kauna ne; kuma wanda yake zaune cikin kauna yana zaune cikin Allah, Allah kuma Yana zaune cikinsa.” (1Yohanna 4 : 16). Mene ne ya fi sanin cewa Allah zai iya zama cikin mutum ta wurin nuna kauna? ’Yan uwana maza da mata bari mu zama masu kaunar juna a koyaushe. kauna halin Allah ne, idan har akwai irin wannan hali a cikinmu, to babu shakka kiyayyar juna ba za ta samu wuri a tsakaninmu ba. Ko cikin iyali, ko wajen sujada, ko cikin kasarmu. Babu wanda zai yi tunanin mugunta ga dan uwansa balle a ce har kisa. Ubangiji Allah Ya taimake mu duka, amin.
kauna (6) Albarkar da ke bin masu kaunar Ubangiji Allah:
A koyaushe Ubangiji Allah Ya zabi Ya yi aiki da mutum ta wurin dangantakar da ke tsakanin Shi da mutum; Shi ne kuma ake ce…