✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kauna (3)

Sanin irin wannan kauna: Ta yaya wani zai san cewa muna cike da irin wannan sahihiyar kauna?Za mu so mu kaunaci wadansu: maganar Allah tana…

Sanin irin wannan kauna:

Ta yaya wani zai san cewa muna cike da irin wannan sahihiyar kauna?
Za mu so mu kaunaci wadansu: maganar Allah tana koya mana cewa “Masoya, idan Allah Ya kaunace mu haka nan, ya kamata mu yi kaunar junanmu. Ba wanda ya taba duban Allah ba dadai; idan muna kaunar junanmu, Allah Yana cikinmu, kuma kaunatasa ta cika a cikinmu: haka nan mun sani muna zaune cikinsa, shi kuma cikinmu, da ya ba mu daga cikin Ruhunsa. (1Yohanna 4 : 11 – 14). Irin wannan kauna ta Allah, idan har akwai ta a cikin mutum, domin daga wurin Allah ne, za mu yi kaunar wadansu mutane, babu yadda za mu zama da kiyayya a cikin zuciyarmu game da kowa; i har da wadanda a ganinmu makiya ne. babu yadda mutum zai iya cewa yana kaunar Allah amma yana zaman gaba da dan uwansa ko makwabcinsa, idan mutum bai kaunaci wanda yake gani ido da ido ba; ta yaya zai ce yana kaunar Allah? Ashe kaunar Allah tana somawa ne da kaunar da muke da shi zuwa ga wadansu.
Zai sa mu dauki mataki ko mu yi wani abu: a cikin Littafin 1Yohanna 3:18 –24, maganar Allah na koya mana cewa “18: ’Ya’yana kanana, kada mu yi kauna da baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.” Sau da dama mutane kan iya cewa suna kaunar mutum a baki kawai; amma cikin zuciyarsu tunanin mugunta ne kawai ya cika; sai ka ga wani yana murmushi da kai, har ka tsammaci cewa wannan mai fara’a ne sosai, ashe daga cikin zuciyarsa ba haka yake ba. “19: Saboda wannan za mu sani muna wajen gaskiya, mu rinjayi zuciyarmu a gabansa kuma.” Idan muna nuna kauna sahihiya, wato ba da baki ba kawai, amma cikin ayukan da muke yi, to, bisa ga maganar Allah muna wajen gaskiya.
Tambaya ta farko ita ce ta yaya mutum zai iya nuna cewa yana da irin wannan kaunar, ba wai fadi da baki ba ne kawai? A cikin 1Yohanna 3:15, maganar tana cewa “Duk wanda ya ki dan uwansa, mai kisan kai ne: kun sani ba mai kisan kai wanda shi ke da rai na har abada cikinsa zaune. In da mun san kauna ke nan, ba da ransa da ya yi dominmu, mu kuma ya kamata mu ba da ranmu domin ’yan uwa.” A wannan zamani da muke ciki, ba abu ne mai sauki ba, ka ga cewa wani ya yarda ya cutu domin wani. Kowa yana son kansa ne kawai da kuma nasa, amma nuna sahihiyar kauna takan soma ne da sanin cewa ba daidai ba ne mutum ya zama da kiyayya cikin zuciyarsa, babu kuma son kai, bari mu sake dubawa a hankali; maganar Allah tana cewa, duk wanda ya ki dan uwansa mai kisan kai ne shi – daga wannan gajeren karatu, za mu gane cewa kashe mutum ba lallai ne sai ka samo takobi ka yanke kan wani ko ka samo bindiga ka harbe wani ba, amma idan akwai kiyayya a zuciyarka game da wani, bisa ga maganar Allah kai mai kisan kai ne. Idan haka ne; masu kisan kai nawa muke da su a yau?
Ta wurin irin bakin halin da muke nuna wa wadansu daga cikinmu, a yau da kyar ne ka samu wanda zai yarda ya sha wahala domin wani ya ji dadi, ko domin laifin wani. kauna irin ta Allah ce kadai za ta iya ba mu izinin yin wannan. Zai zama da ban sha’awa idan har mun iya cire kiyayya daga cikin zuciyarmu, gaskiyar kuma ita ce, za mu iya idan mun sa a cikin zuciyarmu za mu yi. Ikon Ruhu Mai tsarki ne muke bukata mu iya aiwatar da wannan.
Abu na biye kuma shi ne kamar haka “Amma wanda shi ke da dukiyar duniya, yana kuwa ganin dan uwansa da tsiya, ya hana masa tausayi, kaka kaunar Allah za ta zauna a cikinsa?” (1Yohanna 3:17). Idan har Ubangiji Allah Ya albarkaci mutum, sai mu san cewa Allah Yana ganin yadda muke yi da dukiyar da Ya ba mu; mu sani fa Allah Yana ganin komai da muke yi. Sau da dama sai ka ga wadanda suke da shi, ba za su kula da mutane matalauta ba, babu ma ruwansu da mutane da suke shan wahala domin rashi, babu tausayi a cikin zuciyarsu; kuma ba ya damunsu ko kadan cikin lamirinsu. Bari mu ji abin Ubangiji Allah ke fadi a cikin Littafin 1Timothawus 6:17–18; “Ka dokaci wadanda ke mawadata cikin wannan zamani na yanzu, kada su yi girman kai, kada su ratayi begensu bisa wadata mara tsayuwa, amma bisa Allah, Wanda ke ba mu komai a yalwace mu ji dadinsu. Su yi alheri, su zama mawadata cikin kyawawan ayyuka, su kasance da niyyar babbayaswa, masu son zumunta. Suna ajiye wa kansu tushe mai kyau domin lokaci mai zuwa, da za su riski rai wanda shi ke hakikanin rai.”
A cikin tunanin Allah kowane mutum da ke da abin hannu, sai ya tuna da wadanda ba su da shi, ya yi kokari, iya gwargwado, ya yi wa irin wadannan mutane alheri. Nuna sahihiyar kauna ta kunshi bayarwa ga wadanda ba su da shi. Kada ka zama mai rowa, mai son kai mai tunanin gidanka kawai, ka bar arzikin da kake da shi ya gangara zuwa gidajen wadansu da suke cikin mawuyacin hali.
Idan wani ya ce, yana kaunar Allah, kuma yana kin dan uwansa, makaryaci ne shi: domin wanda ba ya kaunar dan uwansa da yake gani, ba ya iya kaunar Allah Wanda ba ya gani. Dole ne mu nuna alheri ga mutane, kada mu yarda Shaidan ya sa mu zama masu rike hannu.
Bin Umarnin Allah: A cikin Littafin 1Yohanna 5:3, maganar Allah ta ce, “Gama kaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinSa: dokokinSa fa ba su da ban ciwo ba.” daya daga cikin manyan abubuwan da zai nuna kaunar da muke da shi ga Allah shi ne yin biyayya ga dokokinSa. Babu yadda za ka ce kana kaunar Allah amma ka ci gaba da aikata abin da ba Ya so, idan kana son ka san matsayinka in ya zo ga kaunar Allah; sai ka tambayi kanka wannan tambaya – shin ina yin biyayya ga maganar Allah kuwa? Ina tafiya bisa ga tafarkin Allah ko kuwa ina yin abin da na ga dama ne kawai?  Yawancin mutane sukan ce suna kaunar Allah, amma rayuwarsu ba abar koyi ba ce ko kadan. Tun ba yanzu da mutane suka koma ga rashin biyayya ga umarnin Allah ba; sun san abubuwan da Allah ba Ya so, amma sun kallafa ransu ga aikata su. Mu tambayi kanmu mu kuma ba da amsa ga kanmu – shin da gaske ne ina kaunar Allah? Yaya rayuwatta take? –Ina rayuwar nan bisa ga maganar Allah ko kuwa bisa ga halin ’yan zamani? Kada ka rudi kanka; abu daya tabbatacce shi ne idan har ka ce kai mai kaunar Allah ne amma ba ka rayuwarka bisa ga maganarSa, kai makaryaci ne, kuma ba ka da mazauni a wurin Allah. Ubangiji Allah Ya taimake mu, amin.