Daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga kan kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi a yankunan Jihar Katsina.
Masu zanga-zangar sun tare hanyar Katsina zuwa Kankara tare da yin kone-kone a garin Marken Dogon Ruwa na Karamar Hukumar Dutsinma.
Suna zanga-zargar ne bayan a daren Laraba ‘yan bindiga sun kai hare-hare a kauyukan Sanawa, Bera, Turare da kuma Dogon Ruwa da ke yankin Makera.
Tuni ‘yan sanda suka isa wurin domin lallashin masu tarzomar su bari a bude hanyar.
Karo na biyar ke nan da mazauna ke yin makamanciyar zanga-zangar sakamakon karuwar ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
Watanni biyu da suka an yi irinta a Daddara da ke Karamar Hukumar Jibia da garin Yantumaki na Karamar Hukumar Danmusa, sai kuma garin Yankara da ke Karamar Hukumar Faskari.