Al’ummar mahaifar tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari da ke Daura a Jihar Katsina sun roki ’yan Najeriya da su yafe masa duk abin da yi musu ba daidai ba a lokacin da yake kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a tsawon mulkinsa.
Buhari dai ya mika wa Tinubu mulki ranar Litinin bayan shekara takwas, kuma shi da kansa ya nemi gafarar ’yan Najeriya a lokuta daban-daban.
- Gwamnan Sakkwato ya soke duk mukaman da Tambuwal ya bayar tun daga watan Maris
- Emefiele ya hadu da Tinubu a Aso Rock
Amma kiran na baya-bayan nan ya zo ne a ranar Talata bayan da Fadar Sarkin Daura, Mai Martaba Sarkin Daura, Umar Umar ta gudanar da wani gagarumin hawan daba domin tarbar Buhari.
An gudanar da bikin ne daga babban titin Garin Daura zuwa shahararren dandalin Kangiwa da ke tsohon birnin Daura a Katsina ta Arewa.
Taron ya samu halartar manyan mutane da suka hada da sabon gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda da aka rantsar; Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum; Sarkin Katsina, Abdulmumini Usman; tsohon shugaban ma’aikata na tsohon shugaban kasa, Ibrahim Gambari; tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika da sauransu.
A yayin bikin, an ga tawagar mahaya dawaki da aka zabo daga masarautun Daura biyar da suka hada da Baure, Daura, Mai’adua da Sandamu, da Zango sun halarci bikin wanda ya dauki tsawon awanni uku ana yi.