✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Emefiele ya hadu da Tinubu a Aso Rock

Tinubu ya sami rakiyar Mataimakinsa da Gbajabiamila

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, yanzu haka yana Fadar Aso Rock don ganawa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu dai ya shiga fadar ne wajen misalin karfe 2:30 na rana.

A ranar Litinin ce aka rantsar da Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya na 16.

Ya sami tarba daga Mataimakinsa, Shettima, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele; Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kyari da Shugaban Majalisar akilai, Femi Gbajabiamila da kuma Babban Sakataren Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Tijjani Umar da Wale Edun da kuma James Faleke.

Aminiya ta gano cewa za a yi tattaunawar ce a kan umarnin da Tinubu ya bayar na daina biyan tallafin mai.