Gwamnatin Jihar Katsina ta ba kungiyar kwallon raga gudunmuwar Naira miliyan 42 don gyara fili da ke kusa da gidan karfe na Katsina.
Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Katsina, Alhaji Aminu Ibrahim Safana ya ce haka a ofishinsa yayin da ake kaddamar da sababbin shugabannin da za su jagoranci kungiyar wasan kwallon ragar ta jihar a ranar Alhamis din makon jiya.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta bunkasa wasan kwallon ragar kamar yadda sauran wasanni ke samun kulawar gwamnati don tafiya da zamani.
Sabon Shugaban kungiyar Alhaji Sada Mohammed Sada ya yi alwashin kawo sauyi a harkar kwallo raga.
“Za mu ci gaba da bunkasa kwallon raga har zuwa sauran kananan hukumomin jihar. Don haka ina fata kananan hukumomi za su kafa kulob-kulob din wasan raga tare da ba su duk tallafin da ya kamata don ciyar da wasan gaba musamman a tsakanin matasa,” inji shi.
Ya nuna damuwarsa a kan irin yadda aka mayar da wasan kwallon ragar baya a kasar nan.
“A kwanakin baya aka kammala gasar wasannin motsa jiki tsakanin kasashe renon Ingila, amma babu wakilcin Najeriya ta fannin kwallon raga, wannan babban kalubale ne.”
Katsina ta farfado da kwallon raga
Gwamnatin Jihar Katsina ta ba kungiyar kwallon raga gudunmuwar Naira miliyan 42 don gyara fili da ke kusa da gidan karfe na Katsina. Kwamishinan Matasa…