Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce katunan zaben mutum 51,373 a Jihar Kano sun lalace bayan an yi musu musu rajista a shekarar 2022 da muke ciki.
Kwamishinan INEC Reshen Jihar Kano, Farfesa Riskua Arabh, ya bayyanna cewa daga watan Janairu zuwa yanzu, hukumar ta yi wa mazauna Jihar Kano 128,628 rijistar zabe, kuma an samu ingantattu guda 77,255 daga ciki.
- Mataimakiyar Shugaban Amurka ta kamu da COVID-19
- Sam ba da Nafisa nake maganar tarbiyya ba – Sarkin Waka
Da yake bayanai a ranar Talata, Farfesa Arabh ya bayyana cewa Jihar Kano ta samu karin rumfunan zabe 3,148, wanda hakan ya kara yawan runfunan zabenta zuwa 11,222.
A cewarsa, hakan yana daga cikin yunkurin hukumar na samar da sauki da takaita zirga-zirgar mutane a lokutan zaben 2023.
Kazalika ya ce akwai katinan rijistar 481,318 sabbi da tsoffi da har yanzu masu su ba su je sun karba ba.
Ya yi wannan bayanin ne a ranar Talata a taron wayar da kai ga ’yan jarida kan rahotan zabe da hukumar ta shirya a Kano.
Arabh ya ce taron an shirya shi ne domin fidda hanyoyin gudanar da zabukan da al’umma suka yarda da ingancinsu.
Ya yi alkawarin ci gaba da gabatar da zauren tattaunawar tare da kira ga wadanda ba su karbi katin zabensu ba da su kokarta su je su karba.
A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) Reshen Jihar Kano, Abbas Ibrahim, kira ya yi ga hukunar da ta ci gaba da shirya makamanciyar wannan ganawa da ’yan jarida,
Ya bayyana cewa sanar da ’yan jarida duk wani sabon bayani da ya kamata su sanar da al’umma dangane da zabe zai taimaka wajen dakile yada labaran bogi.
Wakilin Aminiya ya rawaito cewa fiye da ’yan jarida 20 ne suka halarci taron bitar daga kafofin yada labarai daban-daban.