✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Katin dan kasa: An cafke jami’an NIMC na bogi a Kano

Hukumar mika 'yan damfaran a hannun ’yan sanda don ci gaba da bincike.

Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC), reshen Jihar Kano ta cafke ’yan damfara masu cutar mutane da sunan su ma’aikatan hukumar ne.

An cafke ma’aikatan NIMC na bogin ne a samamen da hukumar ta fara don bankado masu yin aikin rajistar shaidar dan kasa na bogi a Jihar.

“Mun yi cafke wasu mutane da ke damfarar jama’a da sunan su jami’an NIMC ne.

“A kwanaki uku da muka fara bincike a kwaryar birnin Kano, mun gano shagunan intanet da wasu jami’an bogi masu cutar mutane da sunan hukumarmu,” inji Hukumar.

Ta bayyana a shafinta na Twitter cewa an kama jami’an na bogi dauke da katin shaidar ma’aitan hukumar na bogi, takardun yin rijista mallakar lambar dan kasa (NIN), da sauransu.

Ta ce an mika wadanda ake zargin ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, domin fadada bincike kafin a gurfanar da su a kotu.

NIMC ta gargadi ’yan Najeriya da su yi hattara wajen yin rijistar lambar  dan kasa ta NIN saboda kada a damfare su.