Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobin cewa kashin ’yan bindiga ya bushe saboda gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da karfin soja har sai ta ga bayansu, musamman a Arewa maso Yamma.
Ya bayyana hakan ne a Maiduguri babban birnin Jihar Borno, lokacin da ya kai wata ziyarar aiki don kaddamar da wasu ayyuka.
- ’Yan bindiga sun sake tare hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, sun kashe matafiya
- An gano halittar da ta shekara miliyan 66 a cikin kwai tana jiran kyankyasa
Ayyukan dai gwamnatin Jihar da hamshakin attajirin nan dan asalin Jihar, Muhammad Indimi ne suka aiwatar.
Buhari ya ce, “Ina sane matuka da nasarar da muka samu a nan [Arewa maso Gabas], da kuma kalubalen da muke fuskanta a shiyyar da na fito ta Arewa maso Yamma.
“Al’umma daya ne, al’adunsu iri daya ne, suke sassace kayan juna kuma suna karkashe juna. A kan wane dalili?
“Na ba da umarni, kuma tuni mun fara karbar kayan yaki daga Amurka, wadanda suka hada da jiragen yaki da masu saukar angulu da motocin silke, kuma sai mun ga bayansu.
“Babbar matsalar ita ce mun karbi kasar nan a cikin wani mawuyacin hali, ku da kuke Arewa maso Gabas kun fi kowa sani, don kun sha fade a wurare daban-daban,” inji Shugaban Kasar.
Buhari ya kuma sake jaddada cewa zai sauka daga mulki da zarar wa’adinsa ya kare kamar yadda ya yi rantsuwa da Alkur’ani da kuma Kundin Tsarin Mulki.
“Saura wata 17 na tafi, kuma ina fatan duk wanda ya gaje ni ya dora kan muhimman abubuwa ukun da na fi mayar da hankali a kansu, musamman tsaro, saboda in babu shi, babu abin da zai tafi.”