Kungiyar Kasashen Larabawa ta bukaci Isra’ila da ta takatar da kisan gillar da take wa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza.
Sakatare-Janar na kungiyar, Ahmed Aboul Gheit, ya kuma yi tir da hare-haren na Isra’ila, wanda ya a matsayin tsantsar “tauye hakkin Falasdinawa” ne a matsayinsu da ’yan Adam.
- Rikicin Gaza: Ba’amurke ya kashe yaro Bafalasdine dan shekara 6
- Ana zargin matar aure da satar mazakuta a Abuja
Ya bayyana a taron kungiyar a birnin Baghdad na kasar Iraki cewa, “Muna kira ga Isra’ila ta gaggauta janye sojojinta ta bude hanyoyin kai wa Falasdinawa agaji.”
Ahmed Aboul Gheit ya ce yanke ruwan sha da wutar lantarki da man fetur da hanyoyin sufurin abinci zuwa Gaza ba komai ba ne face yunkurin yi wa Falasdinawa kisan kare dangi.
Isra’ila ta kashe Falasdinwa sama da 2,700 cikin mako guda a Zirin Gaza, inda jiragenta suke luguden bama-bamai, sojoji suke kai samame ta kasa.