✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasaitattun wasanni 5 kafin Gasar Kofin Duniya na 2022

Wasanni biyar da ba za ku so a ba ku labari ba a ranar Asabar 5 ga Nuwamba, 2022

Yayin da tawagogin kwallon kafa a fadin duniya ke haramar tafiya Gasar Kofin Duniya a kasar Qatar, ga kasaitattun wasanni biyar wadanda ba za su so a baku labari ba.

Wasannin da za a fafata a yau Asabar 5 ga Nuwamba, 2022, za su kayatar matuka, a yayin da ake shirin rufe gasannin kasashe kafin fara Gasar Qatar 2022 daga ranar 20 ga watan Nuwamba da  muke ciki.

1. Barcelona da Almera

Karfe 7 na yamma (GMT), a Filin wasa na Camp Noua, Spain

Wasan shi ne na karshe da Pique Gerard zai buga wa Barcelona kafin ya yi ritaya. Shi ne kuma wasansa na 616 a gasannin da ya buga a kulod-kulob.

Bayan haka, wasan na Almeria da Barcelona na goge raini ne, Barcelona ke bin Real Madrid da maki daya a teburin Gasar La liga.

Barcelona da Pique na bukatar nasara a wasansa na karshe domin darewa a saman teburin, idan kuma ta sha kaye ta yi kasa.

2. Los Angeles FC da Philadelphia Union

karfe 4 na yamma (GMT) a Filin wasa na Banc of California, a Kalifoniya, Amurka

Wannan shi ne wasan karshe na Gasar Kofin Gasar MLS ta Amurka, kuma da alama zai iya zama wasan da ya fi kownne armashi a cikin ’yan shekarun nan.

Kungiyar Los Angles FC (LAFC) ta zura kwallo shida bayan karin lokaci a wasanni biyu, kuma ba ta taba shan kaye a wasannin da ta karbi bakunci a Gasar Eastern Conference ba.

Sannan, kunnen doke aka tashi a wasanni uku da suka fafata da Philadelphia Union — abokiyar karawarta da za su goge raini a yau.

Sai dai kuma Philadelphia Union kungiya ce mai abin abin ban mamaki a harkar tamola.

Sau 13 Philadelphia Union tana cin kwallo biyu a kasa da minti biyar a gasar MLS ta Amurka, da ke karewa a yau.

3. Atalanta da Npoli

Karfe 5 na Yamma (GMT); a filin wasa na  Gewiss a Bergamo

Napoli, wadda ke kan saman teburin Gasar Serie A da tazarar maki biyar, za ta je gidan Atalanta, wadda ke matsayi na biyu.

Zuwa yanzu, wasa daya tal kowacce daga kungiyoyin ta yi rashin nasara a kakar Serie A ta bana.

Idan Napoli ta yi nasara a wasan yau, za ta kara yi wa Atalanta fintinkau; amma da alama Atalanta ba za ta bari ba, za ta so kamo Napoli, har ma ta sha gabanta a kan teburi daga wasan na yau.

Ganin suna saman tebur, kocin Napoli, Luciano Spalletti, na burin daga kofinsa na farko a gasar ta kasar Italiya a bana; kuma nasararsu a wasan yau zai kara kai shi kusa ga cikar burinsa.

Sai dai akwai jan aiki a gaban Napoli, domin babu kungiyar kungiyar da ta fi karfi wajen tsaron gida a gasar Serie ta kasar Italiya, bayan Juventus.

Yanzu dai ba a san maci tuwo ba.

4. Galatasarya da Besiktas

Karfe 7 na yamma (GMT) a filin wasan na Nef a birin Santanbul, kasar Turkiyya

Idan a wannan karon Galatasaray ta lallasa Besiktas wadda ke samanta a matsayi na daya a gasar Super Lig ta kasar Turkiyya, to ta karo na hudu ke nan Galatasaray tana yin nasara a gidanta.

Hakazalika, idan ta yi nasara, to za ta rage tazarar tsakaninta da Besiktas da maki hudu; amma fa sai idan ta iya keta bayan Besiktas — wadda kwallo 9 aka ci su kawo yazu a gasar.

Zuwa yanzu dai Besiktas ta zura kwallo 25 a wasanni 12 da ta fafata a kakar bana, ga shi kuma dawowar babban kocinta, Senol Gunes, ya kara mata kaimi.

A daya bangaren kuma, dan wasan Galatasaray, Kazimcan Karatas, zai dawo murza leda bayan raunin da ya samu.

5. Manchester City da Fulham

Karfe 3 na Rana (GMT) a Filin Wasa na Etihad.

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ce gwanin cin kwlallo, Earlin Haaland, wanda ya zura kwallaye 22 a bana, zai taka leda, bayan an hutar da shi a wasansu da Sevilla a Gasar Zakarun Turai a makon jiya.

Sai dai kuma har yanzu Kalvin Phillips da Kyle Walker ba su murmure ba, don haka ba za su buga wa kungiyar wasan ba.

A halin yanzu Manchester City ce ke biye da Arsenal da maki biyu a saman teburin Gasar.

Sai dai kuma Fulham wadda a bana aka daga likafarta ta fara Gasar Firimiyar da kafar dama, inda a yanzu take matsayi a bakwai a kan tebur.

Amma dai akwai aki a gaban kocin Fulham, Marco Silva, na tabbatar da ganin kungiyar ba ta barar da duk wata dama da za ta samu a wasansu ba da Man-City ba – wadda ta yi nasara a wasanni 14 da ta karbi bakunci.