✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasafin kudin 2016: Majalisa ta bukaci Hukumar NSC da NFF su gurfana a gabanta

Rahotanni da ke fitowa sun nuna Majalisar Dattijai ta kammala shirye-shiryen gayyatar  Hukumar kula da wasanni ta kasa (National Sports Commission, NSC) da Hukumar shirya…

Rahotanni da ke fitowa sun nuna Majalisar Dattijai ta kammala shirye-shiryen gayyatar  Hukumar kula da wasanni ta kasa (National Sports Commission, NSC) da Hukumar shirya kwallo ta kasa (NFF) don ganin sun kare kasafin kudin shekarar 2016 da suka gabatar a bana.
Shugaban kwamitin kula da harkokin wasanni na Majalisar Dattawa, Sanata Obhinna Ogba ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Talatar da ta wuce a Abuja.
Ya ce kwamituinsa zai ba Hukumomin damar kare kansu ne wajen ganin sun gamsar da majalisar yadda za su kashe kudadensu a kasafin kudin bana ba tare da an samu matsala ba.
“Mun kammala shirin rubuta wasiku ga Hukumomin NSC da na NFF don gayyatarsu zuwa majalisa don su kare kasafin kudinsu a bana.
“Ina tabbatar muku cewa kafin karshen wannan wata ne za mu gayyato hukumomin zuwa majalisa don muna yin duk mai yiwuwa ne wajen ganin mun yi bitar kasafin kudin bana a kan lokaci don ganin ba a samu matsala ba”.
Daga nan ne Sanatan ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buharii a kan karramawar da ya yi wa ’yan wasan Najeriya a makon jiya, inda ya yi musu ruwan kudi a wani taron liyafa da aka shirya musu a fadar gwamnati da ke Abuja a makon jiya.
Ya ce yin haka zai karfafa gwiwar ’yan wasa da ke kasar nan wajen ganin sun cigaba da zage damtse wajen daukaka martabar kasar nan a idon duniya.