Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta ce ta samu nasarar kama wasu motoci guda hudu kirar J5 makare da barasa.
Shugaban Hukumar KAROTA, Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka lokacin da yake duba motocin bayan da jami’an Hukumar suka sami nasarar cafke motocin.
- Abba ya rage wa maniyyatan Kano kuɗin Hajjin bana
- Dole mu ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin ’yan ta’adda — Tinubu
Ya ce Hukumar KAROTA ta sami nasarar kama motocin ne bayan rahoton sirri da ta samu a wajen wasu masu kishin Jihar Kano.
Ya ce dokar Jihar Kano ta haramta shan barasa a kowanne lokaci, musamman yanzu da ake cikin wata mai alfarma na Ramadana.
Ya kara da cewa ya zama wajibi hukumar ta rubanya kokarinta wajen sa ido a daukacin titunan jihar.
A karshe ya yaba wa jami’an da suka sami nasarar cafke motocin, yana mai cewa da zarar an kammala binciki za a mika wa Hukumar Hisbah barasar domin ta kara fadada bincike da kuma daukar mataki na gaba.