Baban-burin-huriyya
A kara kaimin gyara
A dakile masu waftar gara
A gargadi masu kwado da dara
A kyautata Haurobiya
Kuri’unmu an zube
Kai musu kurin zobe
Ko a Jihar Yawon-bebe
Na gaida Makau da Asabe
Kui ta lumanar hana dambe
’Ya’yan danboto
Ku yasar da kwarmato
Saurayin-kirinki ya subuto
Hakkin talaka sai an kwato
Tuni na samu rahoto
Turka-turkar tumurmutse tunkuza
Magabta sun ga haza
Gwarzon gwaraza
Ga gwaza
Baba ya zame musu kazaza
Mui sammako
Mun samu sakamako
Mai mamako
Sai mu kandami koko
Ayyuka su baibaye kowane loko
Jam’iyyar tsintsiya
Kar ai tsiyatakun tsiwar tsiya-tsiya
Karnai na kada wutsiya
Haushinsu sunkutar mikiya
An dai sha kan makiya
An yi zabi-sonka
Saura rikon ragama
A daina duk wata rigima
Aikin gama ya gama
Kowa ya zo mui harka
Masu harkalla
Za a tsabga musu bulala
Sui ta lalala
A halin kila-wa-kala
Sai ma an raba salala
Al’umma ta sha wahala
Sai a sama mata walwala
Kowa-da-kowa a kula
Sai mu sakata mu wala
An kawar da masu gilla
Shirin sharbar shawarma
Sandar samun makama
Daga kasa zuwa sama
Kowa ya kara himma
A bibiyi bukatu masu kima
Kasa ta samu madogara
A daina kara-kara
Laluben damfara
A farga da kamun fara
Kowane kuskure a gyara
Harobiyawa nai kira
Al’umma ban da kangara
A hori masu fandara
Hukunci ba jira
Tsintsiya ai ta shara
A bude kasuwa
A sawo tantakwashin kasusuwa
Ban da dira wawa
Ko hatsaniya da kokowa
Mu ji dadin kai-kawo gari da dawa
Zaman lumana
Ya wanzu a ko’ina
In an hana cin amana
A tarairayi juna
Tare da tarin kauna
Kwakkwafi
Kokarin kofi
Karajin karfi
Kicifin kan karofi
Kutu-kutun korafi
Sakon-dussa
Sarkin-dusa
Sakamakon mai dasisa
Sare-sarin suburbuda tusa
Sarauniyar kisisinar kissa
Asibicin arangamar Arewatawa, Asabe da makau sun maka wa Baban-burin-huriyya marka-markar ruwan kuri’u, inda jam’iyyarsa mai alamar tsintsiya ta tattara ta yi musu kurin zobe, har a Jihar Yawon-bebe, inda Baba ya lula ya yi famfalakin raba ni da man-kaza, mai hankoron tafka TURKA-TURKAR TUMURMUTSE TUNKUZA. Hakika zababbakar zabukan shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa ta kayatar, domin duk wanda ya yi yunkurin kwata tataburzar tabargazar WURU-WURUN-BEBE, tuni ya sha kashi a hannun BABE namijin fara.
Haurobiyawa wadanda zababbakar zabukan wannan shekara ta haifar musu takun-saka da juna, ya kamata a himmatu ka’in-da- na’in wajen tabbatar da wanzuwar zaman lumana a ko’ina, tare da tarairayar juna da tarin nuna kauna.
’Yan makaranta masu falle shafukan mujallu da makalu da baje na-zomo a akwakun batutuwa, lokaci ya yi da za a kara kwazo, amma a rage kwakwazo, wajen kiran kowa-da-kowa ya zo, mu bi zugar gwarzo, wajen hana ALARAMMAN ALMAJIRAN AREWATAWA bin dandazon cin kanzo. Don ta haka ne kawai za mu iya yi wa mazaje kozo. Lallai a kara kwazo. Kai na tuno aminina Yakubu Bazo-bazo.
Tuni dai an hana KUNDUGE KWANGEN KWAGE, don haka kowa ya dage, mu rabarbashi miyar dage-dage. Lallai batutuwa su kasance babu kage. Duk da haka wannan ba ta hana wasan ’yar burun-burun tsakanin bera da mage.
Zan karkare darasin makon nan, ta hanyar zaburar da Baban-burin-huriyya da Usainin-Babajo kan cewa babu hutu, sai ku jajirce wajen tunkarar dimbin kalubalen da ke addabar kasar nan, lallai a warware mana sasarin BANKE BOBO DA KWAMBON BOKOKO, don mu ji dadin kwankwadar KOKO. Hatsaniyar hautsinin Fullo da mai sana’ar na-duke, lamarin tuni ya kuke, kar a bari sarkakiya ta sassarke. A tsarin tsimi da tanadi, wajibi ne a hana TSUWURWURTA TSIMIN TSAMIYAR TA’ADAR TADA ADDAR TA’ADI, lamarin da ya haifar wa al’ummar kasar nan TSININ TSITAKAR GA LUKUDI, GA LAKUME KUDI; kai har ma KUSHEWAR KUDI aka bankado.
Wai na ji SAKON-DUSSA ja-gaban jam’iyya mai danboto da sanda jirge na ta hatsaniyar hargitsa al’umma, inda ya yi nuni da cewa wai TSARINSU NA DAMA-DAMAR-KURDA-KURDAR SIYASAR DAMO-DA-KURA-DA-DIYYA na fuskantar barazana, saboda kawai an yi kokowar kada kuri’u KANEN BABA-OJO ya sha kaye kasa warwas. Wai abin tambaya a nan shi ne, zamanin mulkin mulaka’u na mai danboto da sanda jirge, inda ta shafe shekaru sili da manuniyar sama tana yi wa DAMON-KURAR-DIYA karan tsaye, wane ne ya tuhume su, ko ya jefa musu azargagiyar zargin tafka ta’asa a kwanon tasa? Ko ma dai wacce irin amsa aka bayar game da tambayar da na bijiro da ita, ina jan na-zomon al’umma cewa, “ba ma bukatar Karkarin kokarin kofin kirkirar korafi.” Idan ma kun ki ji, to ba kwa ki gani ba.
Kafin mu fara SHIRIN SHARBAR SHAWARMA, wajibi ne mu daura damarar shawarwari nagari a wajen Baban-burin-huriyya, tare da rokon Mai-duka, Mai-kowa, Mai-komai Ya jibinci lamarinsa, ta yadda zai samu kuzarin kyautata ayyuka. Mu kuwa mu zamo al’ummar da ke karkashin jagorancin NAGARGARU, wadanda suka GYARU, za su MORU, kuma kada a bari kowa ya KWARU.