‘Yan Majalisar Wakilai ta Kasa daga jam’iyyar PDP sun hana Karamin Ministan Mai Dokta Ibe Kachukwu gabatar da jawabi lokacin da ya bayyana a gaban zauren majalisar da ke Abuja, yau (Litinin).
Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ne ya bukaci zaman na musamman saboda janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a makon jiya.
‘Yan jam’iyyar PDP da ke zauren majalisar sun rika daga tutar Najeriya suna cewa: “A’a, A’a. A ceto Najeriya.” lokacin da shugaban majalisar ya bukaci da su yi shuru, su zauna.