An samu karin wasu dalibai uku da suka tsere daga hannun ’yan bindiga bayan sace su a makarantar Sakandiren Bethel Baptist High School ta Kaduna makonni uku da suka gabata.
Aminiya ta ruwaito cewa, daliban sun tsere ne daga wani sansani da ake tsare da su tun a ranar 19 ga watan Yulin 2021.
Wata ’yar uwa daya daga cikin daliban mai suna Funmi ce ta tabbatar da hakan a ranar Litinin.
Funmi ta shaida cewa daliban uku sun shafe kwaki biyar suna yawo a jeji gabanin su hadu da wasu makiyaya da suka taimaka wajen nuna musu hanyar fita.
Bayanai sun ce daya daga cikin daliban bayan shiga gari ya iya tuno lambar wayar mahaifinsa, inda cikin gaggawa ya nemi aron waya ya kira mahaifinsa domin ya zo ya maido su gida.
“An gano yaran ne a kusa da Kasuwar Magani a Yammacin ranar Lahadi sa’o’i bayan ’yan bindigar sun sako daliban makarantar 28.
“Hukumar makarantar ce ta kira surukina ta sanar da mu,” inji ta.
Aminiya ta ruwaito cewa, kafin wadannan dalibai uku, akwai wasu daliban biyu da suka tsere daga hannun ’yan bindigar da jami’an ’yan sanda suka tsinto su a jeji.
A Lahadin da ta gabata ce ’yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban makarantar Bethel Baptist suka sako 28 daga cikinsu.
Tun a ranar 5 ga watan Yuli ne dai ’yan bindigar suka kai hari makarantar da ke hanyar Kaduna zuwa Kachia a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.