Shugaban Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Falasdinawa ‘yan gudun hijira, Philippe Lazzarini, ya ce kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza dole ne ba zabi ba.
Kalaman babban jami’in dai martani ne ga Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda a ranar Litinin ya yi watsi da kiraye-kirayen tsgaita wuta tsakaninsa da Hamas a Zirin Gaza, kungiyar da ya sha alwashin ganin bayanta.
- Kotu ta daure ’yan daudun da suka yi shigar mata da rawa a Kano
- ‘Gwamnatin Tinubu na shirin dawo da farashin Dala N750 kafin Disamba’
A cikin yankin na Gaza dai, kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta ce hare-haren Isra’ila ta sama da kasa a kusa da babban asibitin al-Quds, sun jefa jami’an lafiya gami da dubban Falasdinawa da ke gudun hijira cikin firgici.
Wannan na zuwa ne a yayin da ma’aikatar lafiyar yankin Gaza ta sanar da karuwar adadin Falasdinawan suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila zuwa mutane sama da dubu 8,300, cikinsu kuma har da kananan yara fiye da 3,450.
Tuni dai jami’an Majalisar Dinkin Duniya suka bukaci Kwamitin Tsaro ya sake yunkurawa wajen ganin an tsagaita wuta a Zirin Gaza, a daidai lokacin da hukumar UNICEF ta yi gargadin cewa kananan yara sama da 450 ake kashewa ko kuma suke jikkata duk rana a yankin.