✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ’yan daudun da suka yi shigar mata da rawa a Kano

Hisbah ta lashi takobin yaki da badala a jihar.

Wata Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta yankewa wasu ’yan daudu hukuncin daurin wata uku, bayan sun yi shigar mata don yin rawar ‘karya-kwankwaso’ a wajen bikin uban gidansu.

Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Sani Tamim Sani Hausawa, ta samu matasan ’yan daudun da laifin bayan an karanto musu kunshin tuhumar da ake musu, inda nan take suka amsa.

Sai dai sun roki kotun ta yi musu sassauci.

A nan ne alkalin ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar Naira dubu 10 kowannensu tare da yi musu bulala goma-goma.

Mukaddashin kwamandan hukumar Hisbah na jihar, Dokta Mujahiddin Aminuddin Abubakar, ya ce hukumar ba za ta gajiya ba wajen dakile ayyukan badala, domin aikin hukumar shi ne yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.