Za a koma karatu tsawon kwana hudu, yayin da bankuna da ofisoshin gwamnati za su rage awoyin aiki sakamakon matsalar wutar lantarkin da ta kunno kai a kasar Bangladesh.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin makamashi ke karuwa saboda rikicin Rasha da Ukraine.
- Jamus ta kaddamar da jirgin kasa na farko mai amfani sinadarin ‘hydrogen’ a madadin mai
- Farfesa Maqari ya yi wa ASUU tatas kan yajin aiki
Ragin lokacin dai zai fara aiki ne daga ranar Laraba.
Ana rufe galibin makarantu a Bangladesh ne ranar Juma’a, amma yanzu za a koma rufe su tun ranar Alhamis, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Kasar, Khandker Anwarul Islam, ya tabbatar.
Ya kuma ce bankuna da ofisoshin gwamnati su ma za su rage awoyin aikinsu zuwa awa takwas a kullum, amma za a kyale na masu zaman kansu su sanya lokacin da suka ga dama.
Matsalar wutar lantarkin dai wacce yakin na Ukraine ya haddasa ta kuma jawo tashin farashin kayan abinci da na makamashi a fadin duniya.
Gwamnatin Bangladesh dai a ’yan makonnin nan ta sha daukar matakai domin rage yawan raguwar da asusun ajiyarta a kasashen waje ke ci gaba da yi.
Gwamnatin ta kuma ce tana duba yiwuwar samun makamashi mai rahusa daga kasar Rasha ta hanyar wata sabuwar yarjejeniya da za su kulla.
Sai dai kasar ta yi alkawarin ci gaba da samar da wutar ga yankunan da ke da masana’antu domin tallafa wa tattalin arzikin kasar da ya kai Dalar Amurka biliyan 416.