✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karancin Kudi: Iyalina ba sa iya girki —Orji Kalu

Sanata Kalu ya ce tsarin canjin kudin ya shafe shi ta yadda ba a iya yin girki a gidansa

Sanata Orji Uzor Kalu ya ce sauyin kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shafe shi ta yadda iyalinsa ba sa iya yin girki.

Kalu ya bayyana haka ne cikin wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels kan zaben 2023 da ke tafe, inda ya ce yanzu yana fama wajen samun kudi.

“Idan ka duba za ka ga tsari ne mai kyau, amma ina shan wahala saboda ba na barin kudi a gidana.

“Akwai ranar da manajan gidana ya fada wa matata a Abuja cewa babu kudin da za a yi girki.

“Matata ta shiga damuwa saboda akwai mutanen da nake ciyarwa mutum 250 kullum.

“Wannan matasala ce a gare ni da ma kowa,” in ji Sanata Kalu.

Wannan dai tsari ya sanya gwamnonin APC sanya zare tsakaninsu da Shugaba Buhari.

Hakan ne ya sanya gwamnonin maka Gwamnatin Tarayya da CBN a Kotun Koli suna neman ta hana daina amfani da tsofaffin takardun kudi, inda kotun ta dakatar da shirin gwamnatin kan wa’adin daina amfani da kudi.

Daga bisani Shugaba Buhari ya kara lokacin amfani da tsohuwar takardar Naira 200, amma ya ce wa’adin musayar takardun N500 da N1,000 ya kare tun a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Sai dai ya umarci CBN da ya samar da isassun takardun tsohuwar 200 don ci gaba da amfani da ita zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.

Da yake mayar sa martani kan wannan batu, Sanata Kalu ya bukaci shugaba Buhari da ya mutunta hukuncin Kotun Kolin.

“Ya kamata Shugaban Kasa ya bi umarnin kotu ko da kuwa tana kan kuskure, ya tambayi Antoni-Janar dinsa ya yi masa bayani game da hukuncin kotun kolin.”

Yanzu haka dai Kalu ne Sanatan da ke wakiltar Abiya ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya.