Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce bai kamata ’yan siyasa zargi tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ba don ya goyi bayan takarar Peter Obi.
Shehu Sani ya wallafa hakan ne a shafinta na Twitter.
- Su Obasanjo suka jefa Najeriya cikin tasku —Akinyemi
- Buhari zai sanya hannu kan kasafin kudi ranar Talata
“Obasanjo ya bayyana zabinsa kuma yana da damar yin hakan, bai kamata ake sukar sa ba.
“Wadanda ba sa goyon bayan zabinsa, sai su nemi IBB ko Abdulsalami wadannda dukkaninsu tsofaffin shugabannin mulkin soja ne kuma shugabanni ne, ko kuma a nemi Shugaban Brekete shi ma yana nan,” in ji Shehu Sani.
Idan ba a manta ba, a sakonsa na Sabuwar Shekara, Obasanjo ya bayyana goyon bayan takarar Peter Obi.
Sai dai sakon nashi bai yi wa manyan jam’iyyun APC da PDP dadi ba, lamarin da ya sanya ’yan takarar jam’iyyun na shugaban kasa, Tinubu da Atiku mayar masa martani.
Tinubu ya ce Obasanjo ba zai iya lashe akwatin mazabarsa ba, ballantana ya iya kai Peter Obi ga naasarar lashe kujerar shugaban kasa a zaben da za a yi a watan gobe.