Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta yi kira ga dakaru a kan kada su raga wa ’yan ta’addan da ke tayar da zaune tsaye da kawo cikas a kokarin da ake yi na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasar.
Da yake wannan kira a jawabin da ya gabatar a Sansanin Horas da Sojoji da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ce za a tura wani rukuni na dakaru zuwa wuraren karbar horo akan da yaki da ‘yan ta’adda da makamantansu.
- Mutum 3 sun mutu sakamakon mamakon ruwan sama a Katsina
- An cafke mafarauta kan garkuwa da mutane a Adamawa
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Asabar din da ta gaba ta ce Babban Hafsan Sojin Kasan ya kaddamar da sabuwar bataliya mai lamba 699 da za ta assasa shirin dawo da aminci a kasar nan da aka yi wa lakabi da ‘Exercise Restore Hope II’.
Ya ce nasarar da Rundunar ‘Restore Hope l’ ta samu wajen yaki da matsalar tsaro ta haifar da kirkiro da wannan sabuwar runduna wadda za a bai wa horo na musamman na tsawon makonni 16 don ci gaba da yaki da ta’addanci a fadin kasa.
Babban Hafsan ya ba da tabbacin Sabuwar Rundunar za ta taimaka wajen kawo karshen ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji wadanda suke kawo zagon kasa ga zaman lafiya a kasar nan.
Kazalika, Janar Yahaya ya bukaci duka jami’an da za su jagoranci shirin da su tabbatar an bai wa dakarun horon da ya dace domin inganta kwarewar sojojin Najeriya.
Janar Yahaya ya kuma kaddamar da hasumiya mafi tsayi don bunkasa ayyukan sojoji a Sansanin Horas da Sojojin Najeriya da ke Zariya.
Baya ga wannan, ya kaddamar da shirin dasa bishiyoyi da azuzuwa da sauransu, sa’ilin da ya kai ziyara a Makaranta ‘Yan Sandan Sojoji da ke Basawa a garin na Zariya.