Akwai alamun da ke nuna cewa har yanzu tsuguni-tashi ba ta kare ba game da ranakun da aka tsayar don yin zabubbuka masu zuwa a wannan watan da kuma na gobe, domin kuwa Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa duk da cewa a shirye shi da sauran ma’aikatansa suke don gudanar da zaben a sababbin ranakun da aka tsayar, akwai wasu al’amurra da za su iya sanya sake dage zaben, wadanda kuma ba shi da iko a kansu.
Jim kadan bayan Farfesa Jega ya yi wani taro na musamman da manyan jami’an tsaro na rundunonin askarawan kasar nan ya bayyana cewa, jami’an tsaro ne dai za su iya fayyace sahihancin ranakun da aka tsayar dangane da dacewar yanayin tsaro, domin kuwa har yanzu ana nan ana ta fama da matsaloli iri-iri game da haka a sassa da yawa na kasar nan. Baicin matsalar tsaro wacce ake ganin zai yi wuya a shawo kanta nan da ranar 28 ga watannan, akwai kuma batun katin mai jefa kuri’a na din-din-din, wanda har yanzu ake cewa kashi 20 cikin 100 na adadin jama’ar da ya kamata su mallake shi ba su samu ba, kuma hakan na iya kawo gagarumar cikas ga tsare-tsaren da aka yi, duk kuwa da cewa Farfesa Jega na ganin ana iya gudanar da zaben haka nan.
Akwai kuma wata kulalliya game da aiki da na’urar da za ta tantance inganci da dacewar katin da mai jefa kuri’a a tashoshin zabe, kuma wannan maganar na gaban kotu, ba a san yadda za ta wanye ba domin ita sharia’a sa~anin hankali ce, tamkar mace mai ciki ce, ba a san abin da za ta haifa ba.
Babban abin da ya fi damun jama’a dangane da batun lokutan zabe shi ne, yadda ake ta samun sabani tsakanin furucin Shugaba Goodluck Jonathan, wanda ya jajirce cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a sabuwar ranar da aka tsayar, amma kuma sai ga shi nan take-taken manyan jami’an tsaro na nuna akasin haka, suna kuma cusa kawunansu cikin batutuwan tsarawa da gudanar da al’amuran tsaro a harkokin zabe – abin da ke nuna alamun cewa hukumar zaben na iya rasa ‘yancinta na mai cin gashin kanta da kuma daukar matakan da suka dace ba tare da katsalandan ko kazallaha daga kowa ba.
Ta kowace hanya dai aka kalli wanan al’amari sai a fahimci cewa za a yi amfani da batun tsaro, walau dai don a cusa tsoro a zukatan jama’a ko kuma a yi amfani da tashe-tashen hankulan da ke wanzuwa yanzu haka a wasu sassan Arewacin kasar nan a matsayin hujjar da za ta tilasta sake jirgawa da zaben gaba idan har haka na yiwuwa. Shi ya sa ake ta farfagandar cewa ‘yan ta’addan Boko Haram din da ake da’awar ana daidaitawa a dambarwar da ake yi don kawar da su daga yakin Arewa-maso Gabashin kasar nan sun warwatse, sun kuma fantsama zuwa sassa daban-daban, jira kawai suke yi lokacin zabe ya zo, su tayar da kayar baya.
Amma idan har ana son takura jama’a ne, a hana su rawar gaban hatsi a lokutan zabe, ko kuma a ki sakar masu mara don fitsarewa yayin jefa kuri’a, to fa ba za a so a ga karshen kwaranniyar da ke faruwa yanzu haka ba domin kuwa makiya zaman lafiya za su kai gwauro, su kai mari don ganin abubuwan asshan da ke faruwa a arewa sun ja geza har zuwa lokacin zabe, don hakan ya bayar da damar daukan matakan tsorata jama’a kada su firfito zuwa rumfunan jefa kuri’a. Wannan dai ba sabon abu ne ba, domin kuwa hakan ya faru a wasu muhimman wurare a arewa inda aka tayar da yamutsin da ya jawo hasarar rayuka da dukiya don dai kawai daga bisani a tura dubun-dubatan jami’an tsaro don tsorata jama’a su firgice, su kuma gigice, su gwammace da ma sun yi zamansu a gidajensu don gudun kada a dirka masu dalma a banza, a wofi.
To, amma baicin haka nan kuma shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takaran mukamai daban-daban ba su damuwa wajen ganin cewa sun fadakar da jama’a game da muhimmancin firfitowar jama’a birjik don jefa kuri’a, domin kuwa a ranar zabe masu fitowa ‘yan kalilan ne, wadanda ba su kai ko rubu’in wadanda aka yi wa rajistar ba. Ta ko in aka yi la’akari da batun nasarar zabe, ko samun sukunin inganta hanyoyin gudanar da shi a jihohin Arewa sai a fahimci hakan ya dogara ne ga ‘yan siyasa da shugabanninsu, musamman ‘yan takara, wadanda tilas ne su kasance masu tsananin kishin wadanda suka zabe su, ba wadanda za su zame kajin da za su ci, su goge bakinsu ba.
Yanzu ne lokacin da ‘yan siyasa, musamman na Arewa za su farka, su tashi daga barci mai nauyi don su hada kai, su yi furuci da murya guda wajen sukan lamirin dukkan tsare-tsaren da ake yi don hana ruwa guda gudu da kuma tsiro da wasu al’amuran da za su kawo cikas ga zabubbuka masu zuwa ko kuma sake dage shi zuwa wani lokacin da ba zai da ce ba. Wannan ne kawai hanyar da za a bi a tabbatar da cewa ba a tsallake ranar 29 ga watan Mayu ba, watau ranar da ta zame tilas a rantsar da sabbin zababbin shugabanni don a kaucewa matsalar da za ta haddasa tsananin yamutsi da rudami da kuma rashin tabbas a doron kasar nan. Haka shi ne ya kamata domin ba a jinkira al’amuran yau har sai gobe.