Tsohon Kyaftin din Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, Nwankwo Kanu ya yi rashin daya daga cikin wadanda ke jinya a asibitinsa na kula da masu matsalar zuciya da aka fi sani da Kanu Heart Foundation.
Kanu ne da kansa ya sanar a shafin sadarwarsa na Twitter a makon jiya.
“Na yi babban rashi. Wadda na rasa ita ce Enitan daya daga cikin wadanda suke jinya a asibitin kula da masu matsalar zuciya mallakata,” inji Kanu Nwankwo.
Rahotanni sun nuna saboda shakuwar da Kanu ya yi da Enitan ya dauke ta tamkar ’yar cikinsa da hakan ya sa ya yi matukar kaduwa saboda rasuwarta.