Hukumar Zabe ta Jihar Kano (KANSIEC), ta ce za ta fara sayar da takardar neman izinin takarar shugabancin Kananan Hukumomi daga ranar 19 ga watan Oktoba 2020.
Jaridar Kano Focus ta ruwaito Shugaban Hukumar KANSIEC, Farfesa Garba Ibrahim Sheka na cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar ne a ranar Asabar, 16 ga watan Janairun 2021.
Farfesa Sheka ya ce an bai wa jam’iyyu damar gudanar da yakin neman zabensu daga ranar 12 ga watan Oktoba zuwa 12 ga watan Janairun 2021.
Ya ce jam’iyyu su tabbatar sun kammala cike takardun neman izinin takarar kujerar Shugabannin Kananan Hukumomi 44 na jihar da na mataimakansu, kuma su gabatar da su a babban ofishin Hukumar daga ranar 7 zuwa 13 ga Oktoban bana.
Ya ci gaba da cewa, za a gudanar da zaben ne gabanin masu rike da kujerun na yanzu su kammala wa’adinsu.
Kazalika ya ce dokar Hukumar ta 2002 ta yi tanadin cewa a sanar da ranar zabe kwanaki 21 kafin gudanarsa.
Sai dai ya ce a yanzu an sanar kwanaki 90 kafin gudanarsa ne saboda yawan jam’iyyun siyasa da ake da su a jihar Kano domin samun damar aiwatar da duk wani shiri.