✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

KANSIEC ta raba wa zaɓaɓɓun ciyamomin Kano shaidar lashe zaɓe

NNPP ce ta lashe duka kujerun ƙananan hukumomi 44 da kuma na kansiloli 484 na Kano.

Hukumar Zaɓen Kano KANSIEC ta raba wa sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44 shaidar lashe zaɓe.

Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya miƙa wa sabbin ciyamomin shaidar yayin wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar yau Lahadi a Fadar Gwamnatin Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan takarar jam’iyyar NNPP ne suka lashe duka kujerun ƙananan hukumomi 44 da kuma na kansiloli 484 yayin zaɓen da aka gudanar jiya Asabar.

Ana iya tuna cewa dai jam’iyyu shida ne suka shiga zaɓen da aka yi ta kai ruwa rana saboda umarnin kotuna daban-daban da ke haramta gudanar da zaɓen da kuma wadda ta halasta.

An gudanar da zaɓen ne duk da rashin tsaro daga ‘yan sanda kuma rahotanni na cewa ba a samu tashin hankali ba.

Da yake jawabi yayin miƙa wa zaɓaɓɓun ciyamomin shaidar lashe zaɓe, Farfesa Malumfashi ya shaida musu cewa a yanzu nauyi ya rataya a wuyansu na jibintar lamarin ƙananan hukumomin da suke jagoranci.