✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Shugabannin mahaifar Ganduje sun koma NNPP

Karin shugabannin kananan hukumomin Kano sun sauya sheka daga APC zuwa NNPP

Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, mahaifar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Ganduje, ya sauya sheka daga jam’iyyar zuwa NNPP.

Honorabul Ado Tambai Kwa da taimakinsa, Garba Yahaya Labour, da wasu kansiloli sun sauya sheka zuwa NNPP ne tare da Shugaban Karamar Hukumar Garun-Malam, Mudassiru Aliyu, a ranar Asabar.

Kimanin mako biyu bayan Ganduje, wanda shi ne ya mika wa Gwamna Abba Kabir Yusuf ragamar mulkin jihar ya je jihar inda ya mika wa Abba da jagororin NNPP a Jihar Kano goron gayyata zuwa APC.

Sai dai daga lokacin zuwa yanzu  shugabannin kananan hukumomin APC guda uku ne sauya sheka zuwa NNPP, a cikin mako guda.

Aminiya ta ruwaito yadda Gwamna Abba ya karbi Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa, Auwalu Lawan Aramposu, wanda ya sauya sheka zuwa NNPP.

Wannan kuwa na zuwa ne a yayin da wa’adin shugabannin kananan hukumomin jihar masu ci yake karewa ranar 12 ga watan nan na Fabrairu.

Makonni kadan bayan dan takarar gwamnan Kano na APC kuma tsohon mataimakin Ganduje, Nasiru Yusuf Gawuna ya sha kaye a hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP a shari’ar da APC ta kalubalanci nasarar Abba.

Da yake karbar masu sauya shekar Gwamna Abba ya yaba da basirarsu ta ganin dacewar su shigo NNPP sannan ya yi musu alkawarin samun adalci da kuma tafiya tare da su.