✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Kano ta rufe rumbunan masu boye abinci 5

Hukumar ta ce za ta ci gaba da kai samamen don daidaita farashin kayan abinci a jihar.

Hukumar Karbar Koke-Koke da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), ta kai samame tare da rufe rumbunan ajiye kayan abinci biyar da ke kasuwar Dawanau a Karamar Hukumar Dawakin Tofa.

Hukumar ta gano rumbunan ne, makare da waken suya, alkama da sauran kayan abinci.

Shugaban Hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne, ya jagoranci kai samamen kasuwar sayar da kayan masarufn.

Jami’an hukumar, sun fara da bude wani rumbu mallakin Hamir Investment, wanda ke cike da dubban katan-katan na kayan abinci da suka hada taliya, sukari, taliyar yara da sauransu.

Bayan bincike hukumar ta gano an boye kayan ne don tsauwala wa al’umma a lokacin watan Azumin Ramadana da ke tafe.

Shugaban hukumar, ya ce hukumar za ta ci gaba da kai samame rumbunan da ake boye kayan abinci don jefa al’umma cikin tsaka mai wuya.

Hukumar ta kuma rufe wani katafaren rumbun ajiya da aka makare shi da kayan abinci.

Rumbun wanda mallakin kamfanin Rigasa ne, wanda shugaban kamfanin Muhammad Ahmad ya shaida wa hukumar cewa ba boye kayan abinci suke yi ba.

Ya bayyana cewar Majalisar Dinkin Duniya ce, ta bai wa kamfanin kwangilar raba kayan abinci ga jihohin Borno Yobe da Adamawa.

Ya ce sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da kayan abinci amma sun yi asarar sama da Naira miliyan 300 sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a yanzu.

Sai dai Muhuyi, ya bukaci shugaban kamfanin ya gabatar da takardun shaidar yarjejeniyar da ya kulla game da samar da kayan abincin.

Ya kara da cewa hukumar ta samu nasarar gano ma’ajiyar ne, biyo bayan samun bayanan sirri daga jami’an tsaro.

“Aikinmu ya yi tasiri wajen daidaita farashin kayayyakin masarufi. Cikin mako guda farashin shinkafa ya tashi daga Naira 52,000 zuwa 61,000.

“Shi ya sa muka tashi tsaye wajen daukar mataki don dakatar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi. Idan muka dore a haka cikin kankanin lokaci zamu iya rage farashin kayayyaki,” in ji shi.

“Duk rumbun ajiyar da muka shiga sai su ce kayan tallafin agaji ne. Mun yi mamakin yadda abincin agaji zai jefa kasar nan cikin yunwa,” in ji Rimin Gado.

“Ina tabbatar muku da cewa bayan kammala bincikenmu za mu shigar da karar a gaban kotu kuma kotu za ta yi aikinta.”

Rimin Gado ya kuma kai ziyara kasuwar Singa, inda ya tattauna da shugabannin kasuwar don nemo hanya wajen magance tashin farashin kayayyakin abinci a jihar.

A ranar Alhamis ne shugaban hukumar, ya yi barazanar saka kafar wando daya da ‘yan kasuwar da ke boye kayan abinci da nufin sanya kayan abincin yin tsada a jihar.