✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano Pillars ta yi tankade da rairaya

kungiyar Wasan kwallon kafa ta Kano Pillars ta bayar da sanarwar sallamar ‘yan wasa goma daga cikin ‘yan  wasan kungiyar.Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar…

kungiyar Wasan kwallon kafa ta Kano Pillars ta bayar da sanarwar sallamar ‘yan wasa goma daga cikin ‘yan  wasan kungiyar.
Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar Rilwanu Idris Malikawa ya bayyana Aminiya cewa an sallami ‘yan wasan ne saboda matsaloli na rashin lafiya da kuma gazawa wajen yin abin da ya kamata a kakar wasanni da ta gabata.
Idris Malikawa ya ce yanzu haka masu horar da ‘yan wasan kungiyar da kuma shugabanin kungiyar sun yi nisa wajen tattaunawa da wasu kwararrun ’yan wasa daga sassan kasar nan domin cike gibin ‘yan wasan da aka sallama.
Yanzu haka kungiyar na ci gaba da daukar horo a filin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a birnin Kano kuma ya ce an baiwa ‘yan wasan da har yanzu ba su dawo ba da su tabbatar sun yi haka zuwa ranar  Lahadi  don su kasance cikin ‘yan wasan da kungiyar za ta yi wa rijista a kakar wasan da ake sa ran za a fara a ranar 31 ga wannan watan.
  A wani labari makamancin wannan, Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Babaganaru Muhammad ya sake sanya hannu domin ci gaba da aikin horar da ‘yan wasan kungiyar tsawon shekara daya. Babaganarun ya sanya hannun ne bayan da ya gudanar wani taron sirri da shugabannin hukumar gudanarwa  na kungiyar.
Da yake jawabi bayan sanya hannun Babaganaru ya bayyana cewa ya sake sanya hannu ne  domin ya sake bayar da gummawarsa wajen dawo da martabar kungiyar ta Kano Pillars.
A cewarsa  ganin yadda kungiyar ta kare a matsayin ta takwas a kakar wasanni da ta gabata ya ce a bana akwai  shirin da yake yi domin ganin kungiyar ta zama zakara a karshen gasar. Ya gode wa gwamnati da al’ummar Jihar Kano da ma dukkan magoya bayan kungiyar saboda irin gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban kungiyar.