✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Kundin shari’ar Kotun Daukaka Kara ya tabbatar da nasarar Abba —Dederi

Lauyan NNPP ya bayyana cewa nasarar Abba da kundin shari'ar ya fito da shi kuskure ne

Kundin hukuncin shari’ar zaben gwamnan Kano da Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta fitar ya haifar da rudani.

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano Haruna Isa-Dederi ya ce kundin shari’ar ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir na Jam’iyyar NNPP sababin abin da aka sani cewa ta kwace kujerarsa.

A jawabin da ya yi a daren Talata bayan fitowar ainihin kundin hukuncin, Isa-Dederi wanda shi ne Antonin-Janar na jihar ya ce kundin hukuncin ya yi fatali da hukuncin kotun korafin zabe da ta kwace kujerar Gwamna Abba, a matsayin mara hujja.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito kwamishinan na bayyana wa manema labarai cewa, “Shafi na 67 kundin hukuncin kotun daukaka karar da aka fitar ranar Talata dauke da sa hannun Magatakardan Kotun Daukaka Kara, Jameel Ibrahim Umar, ya nuna kotun ta tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen zababben Gwamnan Kano.”

A ranar Juma’a 17 ga Nuwamba, 2023 ne Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta kori karar da Gwamna Abba ya daukaka game da kasancewarsa dan jam’iyyar NNPP kafin zaben 2023 da ake takaddama a kai.

A hukuncin da kotun ta sanar a ranar ta bayyana Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano na ranar 25 ga watan Maris, 2023, bisa hujjar cewa Abba ba dan NNPP ba ne.

Kotun ta yanke hukuncin ne bisa hujjar cewa babu sunan Abba a kundin rajistar mambobin NNPP da Jam’iyyar ta gabatar wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) gabanin zaben da ake takaddama a kai.

A kan haka ne Abba da NNPP suka nuna rashin gamsuwarsu da kuma shirin daukaka kara zuwa Kotun Koli domin kalubalantar hunkuncin kotun daukaka karar.

Sai dai bayan fitowar ainihin kundin hukuncin mauke da sa hannun wadanda suka kamata a ranar Talata, Isa-Dederi, ya ce rubutaccen hukuncin ya nuna kotun daukaka karar ta soke hukuncin kotun sauraron korafin zabe da ta kwace kujerar Gwamna Abba ta.

A cewarsa, kotun da kuma ci APC tarar Naira miliyan daya

wannan kuma ya saba da abin da alkalan kotun suka karanta a yayin zaman shari’ar na ranar Juma’a, wanda  hakan kuma ya tabbatar da Abba Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

Kuskure ne —Lauyan NNPP

Sai dai kuma daya daga cikin lauyoyin da suka halarcin zaman kotun daukaka karar, Barista Abba Hikima ya bayyana cewa abin da ke cikin kundin hukuncin da ke tabbbatar da nasarar Gwamna Abba kuskure ne.

Ya kara da cewa hasali ma, duk sauran bangarorin da ke cikin kudin hukuncin sun nuna cewa kotun ta yi watsi da karar da Abba Kabir Yusuf ya daukaka zuwa gabanta.

Barista Abba Hikima yya ce, “A fahimtata wannan kuskure ne kotun daukaka kara ta yi. Da wuya ka dauki hukuncin kotu ka karanta ba ka samu kuskure ba.

“Ba a zabar wani bangare na hukunci a karanta a manta da sauran. A wannan hukuncin duka sauran bangarorin hukuncin ya nuna AKY bai yi nasara a ‘Appeal’ ba.

“Saboda haka, ba za a dauki wata sadara daya a tsaya a kanta ba. Wannan abu sannane ne a doka kuma doka ta yi tanaji na a abun da ake kira “Slip Rule” wanda shi ne idan an samu kuskure ko tuntuben alkalami a hukunci, to kotu na iya gyara wannan kuskuren musamman idan ma’anar hukuncin ta bayyana.

“Saboda haka, gara a ba wa ainihin dalilan daukaka wannan kara muhimmanci fiye da wannan.”

Ya ci gaba da cewa gara ma Abba da masu kare shi su mayar da hankali kan bangarorin da suka fi muhimmanci wajen daukaka kararsu zuwa Ko, maimakon a kan kuskuren da Kotun Koi za ta gyara.