✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPP ta shirya kawance da jam’iyyun adawa

Jam'iyyar ta ce tana nazarin yadda siyasar kasar nan ke tafiya

Jam’iyyar NNPP ta ce a shirye take domin yin hadaka da kowace jam’iyyar adawa kamar yadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bukata.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Abba Kawu Ali, a cikin wata sanarwa ya ce kiran da Atiku ya yi abin yabawa ne da kuma maraba.

Sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Talata ta ce irin wannan shiri da aka yi ne ya bai wa jam’iyyun adawa a 2015 damar hadewa suka kayar da jam’iyyar PDP mai mulki a lokacin.

“Tabbas kofarmu a bude take ga hadin wannan gwiwa ko kawance da duk wani shiri da bangarori ko jam’iyyun PDP da LP da APC, muddin hadin gwiwar ko tsarin zai amfani al’ummar Najeriya da kuma tabbatar da dimokuradiyyar kasar,” in ji shi.

Ali ya kara da cewa a halin yanzu NNPP “tana nazarin yanayin siyasar kasar nan,” kuma “za ta yi maraba da kowace jam’iyyar siyasa da duk wani shiri ko tayin tattaunawa da nufin kare al’ummarmu, dimokuradiyyarmu da kuma samar da ci gaba mai dorewa a kasarmu.”

A makon da ya wuce ne Atiku Abubakar ya nemi hadin kan jam’iyyun siyasa wajen hadewa domin yakar jam’iyyar APC mai mulki.