✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano da Bauchi sun lashe Gasar Alkur’ani ta Kasa ta 2023

Malama Zainab Aliyu daga Jihar Kano ce Gwarzuwa a bangaren mata, sai Alaramma Ibrahim Muhammad daga Bauchi a bangaren maza

Malama Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano ta zama Gwarzuwar Gasar Alkur’ani ta Kasa ta shekarar 2023 a bangaren mata a hadda da tafsiri.

A bangaren maza kuwa, Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir daga Jihar Bauchi ne ya zama Gwarzon Shekara a musabakar karo na 38, wadda aka kammala a Jihar Yobe.

Mai Masaukin Baki, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karamma Malama Zainab Aliyu Muhammad daga Jihar Kano da kyautar mota kirar Honda Accord.

Alaramma Ibrahim Muhammad Nasir kuma gwamnan ya gwangwaje shi da kyautar mota kirar Honda Accord.

Sannan ya ba da kyautar bas mai daukar mutum 18 kirar Toyota Hummer ga Kwamitin shiryar musabaka na Kasa don ci gaba da dawainiyar gasar Alku’rani.

A ranar Asabar din nan aka kammala Gasar Karatun Alkur’anin ta Kasa karo na 38 a Damaturu, fadar Jihar Yobe inda alarammomi daga sassan Najeriya suka nuna bajintarsu.

A lokacin rufe gasar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yaba wa matasan da suka shiga wannan gasar ta Karatun Alkur’ani Mai Girma rukuni-rukuni, sannan ya yi musu fatan alheri.

Sarkin Musulmi, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya nuna farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da gasar a Yobe cikin kwanciyar hankali kuma a bisa tsari ba tare da an samu cikas ba.

Shi ma Shugaban Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Sulaiman Bilbis ya yaba wa gwamna Mai Mala Buni bisa yadda ya dauki nauyin gasar da kuma yadda aka gudanar da ita cikin nasara.

Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Danfodiyo ne dai ke shirya Gasar Alkur’ani ta Kasa a Najeriya, kuma wanan shi ne karo na 38.

Mahalarta bikin rufe gasar ta Alkur’ani sun hada da Gwamna Jihar Gombe, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, Mataimakin Gwamna Jihar Borno, Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba.

Sai masu girma sarakunan Jihar Yobe gaba daya, karkashin Mai Martaba Sarkin Fika, sai Mai Martaba Shehun Dikwa da ya wakilci Mai girma Shehun Borno, sai Mai girma Sarkin Bauchi da sauran manya-manyan baki.