An nada Barista Aisha Ahmad Muhammad a matsayin “Khadimatul Qur’an” wato Mai Hidimar Al-Kur’ani mace ta farko arko a birnin Zazzau.
An yi wannan nadi ne a wajen musabakar Alkur’ani Mai Girma da ya gudana a dakin taro na Kongo a Tudun Wada da ke Karamar Hukumar Zariya.
Musabakar wadda aka gudanar da ita karkashin jagorancin makarantar Ummul Qura Litahfeezil Qur’an Wata’alimih da ke Zariya, ta sami halartar makarantun Islamiya da na Haddar Qur’ani da dama, inda aka shafe kwanaki hudu ana gudanarwa, kafin a fitar da zakaru.
Shugaban kwamitin Masabakar, Gwani Abdulkareem Ibrahim Paki, wanda tsohon Gwarzon Musabakar Karatun Alkur’ani ne na kasa, kuma ya wakilci Nijeriya a Musabaka ta Duniya a shekarar 2023, shi ne ya jagoranci nadin.
- Matatar Dangote: Ku zo ku saya ku yi yadda kuka ga dama —Dangote ga NNPCL
- An kama su kan tono gawar dan maƙwabcinsu domin tsafi
Ya ce an tabbatar da nadin ne bisa sahalewa da amincewar Majalisar Malamai da Limamai da Makarantun Islamiyya na Zariya sakamakon gagarumar gudumawar da Barista Aisha Ahmad Muhammad take bayarwa wajen yi wa Addinin Allah da Alkur’ani Hidima.
A cewarsa, tana tallafawa ta hanyar raya masallatai da makarantun Islamiyya tare da zamowa kan gaba wajen duk wata hidima ta Alkur’ani da addinin Musulunci.
Gwani Ibrahim Paki ya kara da cewa hakan yana cikin dalilan da aka zabe ta a matsayin wacce ta fi kowa bayar da gagarumar gudummawa ta fuskar daukaka addini da karfinta da kuma aljihunta a cikin mata da ke Karamar Hukumar Zariya.
Shugaban makarantar Ummul Qura ya zayyano wasu daga cikin ayyukan da sabuwar Khadimatul Qur’an din tayi a baya da suka hada da daukar nauyin karatun Dalibai Mahaddata Alkur’ani a makarantun Islamiyya da na hadda a wurare daban-daban.
Sai kuma tallafa wa makarantun Islamiyya da na haddar Alkur’ani da gudumawar K’kudade da kayan karatu sai butoci, gyara da sabunta masallatai da dama a sassan karamar hukumar, tare da daukar nauyin dalibai musamman mata don ci gaba da karatunsu.
Gwani Paki ya kuma yaba da yadda take baiwa zakarun dalibai gudumawar manyan kudade da daukar nauyin karatu don sake karfafawa yara mata gwiwa, a duk duk wata masabaka ko taron addini.
Da take magana da manema labarai jim kadan bayan nadin, Barista Aisha Ahmad Muhammad wadda har ila yau ita ce Sakatariya kuma Mai Bada Shawara ta Fuskar Shari’a a Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna ta yi godiya ga Allah bisa wannan karamci da girmamawa da aka yi mata.
Tace duk da akwai wadanda suka fi ta, amma za ta yi iya kokari wajen ci gaba da bayar da gudunmawarta don daukaka kalmar Allah a duk inda ta sami kanta.
Aisha ta ce yanzu haka ta bayar da kyautar filaye don gina masallatai da makarantun Islamiyya sama guda 20.
Ta ce yara mata wanda ta tallafa masu a harkar karatu sun kai sama da dubu guda.
Daga nan sai ta sha alwashin ci gaba da kokari wajen duk wata harka da shafi addini da kuma inganta rayuwar al’umma ta kowace fuska.
Ta roki ‘yan uwanta mata da su zage damtse wajen tallafa wa rayuwar al’umma ganin irin halin rashi da ake ciki a yanzu.
A karshen taron, ta raba kyautar kimanin Naira miliyan daya da rabi ga wadanda suka yi nasara a gasar musabakar.