Alaramma Abdulhalim Yunus da Malama Amina Idris Tahir sun zama Gwarazan Shekara na Gasar Alkur’ani na shekarar 2024 a Jihar Kogi.
Alaramma Abdulhalim Yunus shi ne Gwarzon Shekara a bangaren masa ’yan Izu Sittin da Tafsiri a musabakar, a yayin da Malama Amina Idris Tahir ta zama Gwarzuwar Shekara a bangaren mata.
Mahaddata Al-Kur’ani 97 daga kananan hukumomi 21 na Jihar Kogi ne suka fafata a wanna musabaka, inda suke baje kolin karfin hadda da tajwidi da kuma sanin ma’anar ayayoyin Alkur’ani.
An shafe kwana biyar mahaddata Al’kur’ani suna gwada bajintarsu a wannan musabaka a matakai biyar.
- Lakurawa: Yadda sojoji ke aiki don murkushe ’yan ta’adda
- Sauya dokar haraji: ’Yan Arewa a majalisa sun nuna damuwa
- Gwamnatin Obasanjo ce ta kafa tarihin cin hanci mafi muni a Najeriya — Fadar Shugaban Ƙasa
Wadannan suka zama gwarazan shekara a kowane mataki su ne za su wakilinci Jihar Kogi a Gasar Musabakar Alkur’ani na Kasa da ke tafe.
Masabaqar wadda ita ce karo na 33 da Jihar Kogi ta gudanar garin Ife Olukotun da ke Karamar Hukumar Yagba ta Gabas ce ta zama mai masaukin baki.
A ranar Lahadi aka kammala tare da rufe musabakar, wadda aka fara a ranar 13 ga wannan wata na Nuwamba, ina alkakai sukan sanar da Alaramma Abdulhalim Yunus da Hafiza Amina Idris Tahir matsayin Gwarazan wannan shekara.