✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gasar karatun Alkur’ani a Adamawa

An gudanar da taron ƙaddamar da gasar Al-Kur'ani ne a ranar 25 ga Nuwamba, 2024, a Massallaci na Daya Nasarawa Demsa

Majalisar Masarautar Demsa karkashin jagorancin Mai Martaba Hamma Batta, Homun Alhamdu Gladson Teneke, ta ƙaddamar da Gasar Karatun Alkur’ani na jihar Adamawa karo na 39 a hukumance.

An gudanar da taron ƙaddamar da gasar Al-Kur’ani ne a ranar 25 ga Nuwamba, 2024, a Massallaci na Daya Nasarawa Demsa.

Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanda Kwamishinan Ƙananan Hukumomi Alhaji Yayaji Mijinyawa ya wakilta ya yaba wa majalisar Masarautar Batta bisa gudanar da karɓar baƙuncin Musabaƙar.

Fintiri ya bukaci mahalarta gasar da su rika bin ka’idojin gasar, inda ya jaddada cewa irin wadannan abubuwan suna inganta haɗin kai da kuma cusa al’adar neman ilimin addini.

Shugaban kwamitin gasar, Alhaji Aliyu Adamu Samaila Numan, ya nuna jin daɗinsa ga waɗanda suka halarci taron, ya kuma yaba wa majalisar ta Batta bisa jajircewar da suka yi wajen gudanar da taron.

Uban taron wanda Hakimin Kawon Dowaya Alhaji Isah A. Zurah ya wakilta, ya jaddada muhimmancin inganta haɗin kai da kuma koyar da ilimin addini ga matasa.

Taron buɗe gasar ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da Shugaban Majalisar Musulmi, Mallam Gambo Jika da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa Mallam Bashir Ahmad.

Taron ya kunshi karatun kur’ani mai tsarki da kuma ta gadin wurin gasar.