✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta kara kasafin 2024 zuwa tiriliyan 28.7

Majalisar ta kara kasafin da tiriliyan 1.2 ta kuma kara farashin canjin Dala da yawan danyen mai da za a rika hakowa

Majalisar Dattawa ta amince da tiriliyan N28.7 a matsayin kasafin 2024, bayan nazarin rahoton kwamitinta na kasafin kudi.

A ranar Asabar din nan ne Majalisar Dattijai ta amince da kashe jimillar Naira tiriliyan 28.78, baayta kara kasafin da Naira tiriliyan 1.2 a kan tiriliyan 27.5 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata watan jiya.

Kazalika Majalisar ta daga farashin canji Dala daga N750 zuwa N800 da hako gangar danyen mai miliyan 1.78 a kullum a kan farashin Dalar Amurka 77.96 kowane ganga.

Majisar ta kuma yi hasashen karuwar kashi 3.88 cikin 100 na kayayyakin da ake samarwa a cikin gida daga abin da bangaren zartarwa ya gabatar.

Daga cikin kasafin na Naira tiriliyan 28.78, Naira tiriliyan 1.74 su ne kudaden dole da za aba wa hukumomin gwamnati; tiriliyan 8.77 na ayyukan yau  da kullum; tiriliyan 9.99 manyan ayyka; tiriliyan 8.27 kuma na biyan bashi

Dalilin damuka kara kasafin 2024 da N1.2trn —Majalissar Wakilai

Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar (APC, Kano) ya bayyana cewa sun kara kasafin da Naira Tiriliyan 1.2 ne saboda hauhawar farashin kayayyaki da kuma alkawarin da Kamfanonin Mallakan Gwamnati (GOEs) na kara kudaden shigansu zuwa Naira biliyan 700.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen gabatar da kudirin kasafin kudin a taron hadin gwiwarsu ranar Asabar, inda ya ce, “akwai hauhawar farashin kaya da kuma canjin dala, sannan bangaren zartarwa yana maganar canjin Dala a kan N750, amma bayan mun yi nazari, sai muka ga hakan ba mai yiwuwa ba ne.

” Don haka muka karu zuwa N800. Kuma mun yi taro tare da GOEs, kuma sun amince su kara musu kudaden shiga yadda za mu iya samun waccan tiriliyan 1.2.

“Wannan shi ne karo na farko manyan ayyuka suk fi na yau da kullum samu kudade. Mun ware wa ilimi Naira biliyan 850; Na yi imanin da wannan kasafin ‘yan Najeriya za su ga tasiri mai yawa”