✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai kamshin gaskiya a kalaman Ningi kan cushe a Kasafin Kuɗi —BudgIT

BudgIT ta ce akwai sassan Kasafin Kuɗin da babu wani gamsasshen bayanin kamawa a ciki.

Wata ƙungiya mai nazari kan kasafin kuɗi da bayanai (BudgIT) ta ce akwai alamun gaskiya kan batun cushen kuɗi da Sanatan Bauchi ta Tsakiya Abdul Ningi ya ce an yi a kasafin 2024.

Daraktan BudgIT, Seun Onigbinde ne ya bayyana hakan a ganawarsa da gidan Talabijin na Channels ranar Laraba.

Ya jaddada cewa Sanata Ningi yana da gaskiya domin akwai wuraren da a kasafin babu gamsasshen bayani kan kuɗin da aka ware da kuma abin da za a yi da su.

Idan za a iya tunawa dai an dakatar da Sanata Ningi ne ranar Talata, bisa zargin da ya yi na cewa a halin yanzu ana amfani da Kasafin Kuɗi iri biyu a Najeriya.

Tun da farko Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na majalisar, Sanata Olamilekan Adeola daga Jihar Ogun ya gabatar da ƙorafi kan tattaunawar da Sanata Ningi ya yi da BBC Hausa, inda ya soki lamarin.

Tun kafin hukuncin da majalisar ta ɗauka, Sanata Ningi wanda ya yi ƙoƙarin kare kansa, ya ce ba a fahimci kalaman nasa ba.

Bayan doguwar muhawara da Sanatocin suka yi kan lamarin, Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, ya ce, an dakatar da Sanata Ningi na tsawon watanni uku kuma an cire shi daga dukkan ayyukan majalisar na tsawon watanni uku masu zuwa.

Tuni dai Sanata Ningi ya rubuta takardar murabus a daga matsayinsa na Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa, yana mai miƙa godiyarsa ga mambobin ƙungiyar da suka ba shi damar jagoranci na tsawon watanni takwas.

Da yake tsokaci kan batun, Daraktan BudgIT ya ce akwai sassan Kasafin Kuɗin da babu wani gamsasshen bayanin kamawa a ciki.

Onigbinde ya ce ware wa Majalisar Tarayya, da Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa, da Hukumar Zaɓe, da Asusun Tallafawa Jami’o’i na daga cikin wuraren da babu wani gamsasshen bayani a kansu, duk da cewa mutane na da haƙƙin sanin halin da ake ciki kan kuɗaɗen da yadda ake kashe su.

“Wajen Naira tiriliyan 2 na kasafin da shugaban ƙasa ya sanya wa hannu ya tafi ne ga hukumomin gwamnati.

“Don haka idan Sanata Ningi ya ce an yi cushe to tabbas gaskiya ne. Domin kuwa ya sha bambam da kasafin kamfanoni mallakin gwamnati da aka ƙara daga baya.

”Ya kamata mu san yaya ake kashe kuɗin TETFUND? INEC ma na karɓar maƙudan kuɗi amma babu bayanin yadda take amfani da su. Haka ma NJC da ita kanta majalisar,” in ji shi.