✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin titin tiriliyan 16 ya yi layar zana a kasafin 2025

A watan Mayu ake sa ran a buɗe yankin katafaren titin da ya tashi daga Sakkwato zuwa Badagry

Aikin titin Legas zuwa Kalaba da Gwmanatin Tarayya ta ce za ta gina a kan Naira tiriliyan 16 ya yi bayan dabo a kasafin kuɗin shekarar nan ta 2025 da Shugaba Bila Tinubu ya aike wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa.

Wanna na faruwa ne a yayin da ake sa ran a watan Mayu wannan shekarar gwamnatin za ta buɗe wani sashe na katafaren titin da ya tashi daga Sakkwato zuwa Badagry da ke Jihar Legas,  kamar yadda Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi ya sanar a watan Disambar 2024.

Sai dai kuma duk da haka gwamanti ba ta fayyace hanyoyin da za ta samu kuɗaɗen aiwatar da wannan gagarumin aikin titi ba. Hasali ma ba a ambace shi a kasasfin 2025 da ke gaban majalisar dokoki ba a halin yanzu.

Aikin mai tsawon kilomita 700, wanda gwamnatin Tinubu ke bugun ƙirji da shi ya haifar da ce-ce-ku-ce, ganin cewa ba a taba aikin titi da ya ci kuɗi kamansa ba a tarihin Najeriya.

’Yan Najeriya sun yi ta ɗaga kara gane da inda za a samo kuɗin aikin, wanda sa farko Gwamantin ta ce za gina ne karkashin tsarin haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP).

 

A watan Fabrairun 2024 ne Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta sahale fitar da Naira tiriliyan guda domin kashin farko na aikin.

Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya bayyana cewa cewa rukunin farkon mai tsawon kilomita 47.7 zai kasance mai ɗaukar motoci biyar a kowanne hannu da kuma titin jirgin ƙasa a tsakiyarsa.

A watan Oktoba ministan ya sanar cewa an ba wa kamfanin High Tech Construction African Limited, a bisa tsarin samo kuɗi da sayen kaya da kuma giwa, kuma ta fara neman kuɗin, amma akwai ’yan matsaloli, don haka muka sake komawa ga shugaban ƙasa muna neman a hanzarta aikin.

“Da haka ne muna ba da shawarar gwamnati ta biya Naira Naira tiriliyan 1.067 na kashin farko mai tsawon kilomita 47.7 wanda ta fara da Titin Ahmadu Bello zuwa Tasha Jiragen Ruwa ta Lekki, kuma shugaban ƙasa ya amince.”

A watan Disamba ne dai ministan ya bayyana cewa a watan Mayun 2025 za a ƙaddamar da wani sashe na katafaren titin da ya tashi daga Sakkwato zuwa Badagry da ke Jihar Legas.

Sai dai kuma gwamanti ba ta fayyace hanyoyin samun kuɗaɗen aikin titi ba, kuma ba ta ambace shi a kasasfin 2025 da ke gaban majalisar dokoki ba a halin yanzu.

Daftarin kasafin na 2025 ya ware Naira tiriliyan 1.065 ga Ma’aikatar Ayyuka amma kuma babu aikin titin na Legas zuwa Kalaba a cikin kasafin, lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Kungiyar BudgIT mai fafutikar da ke bibiyar ayyuka ta intanet, ta bayyana cewa, “tsallaken ya ta’azzra damuwar da ake da ita ga make da ita kan yadda za a samu kuɗin aikin, wanda ake fargabar zai iya sa a karkatar da kuɗaɗen wasu ayyukan zuwa gare shim wanda hakan zai kawo naƙasu ga kasafin da kuma aiwatar da shi.”

Sanarwar da kakakin BudgIT, Nancy Odimegwu, ta snaya wa hannu ta ƙara da cewa wasu abubuwan da ke ƙunshe cikin daftarin kasafin ba masu yiwuwa ba ne, sannan ta soki Gwamnatin kan rashin ba da cikakken bayani kan kasafin ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati.

BudgIT sun bayyana damuwa cewa a shekarun baya an samu cushe a kasafun kuɗi a majalisa, saɓanin aikin da doka ya ba ta, inda ta “riƙa ba wa wasu cibiyoyin gwamnati waɗanda ba su da ƙarfi ko hurumin gudanar da ayyukan.”

Sun bayyana cewa a shekarar 2021 an yi cushen manyan ayyuka 5,601, ina da 2022 ya ƙaru zuwa 6,462 a ma’aikatu 37 da cibiyoyin gwamnati 340. A 2024 adadin ya ƙaru zuwa 7,447 waɗanda kuɗinsu ya kai Naira tiriliyan 2.2.

BudgIT ta ce duk da cewa kundin tsarin mulki ya ba wa Majalisa hurumin ware kuɗaɗe, majalisar tana yawan sauya kasafin da ɓangaren zartaswa ya gabatar wanda hakan ke cin karo da ainihin manufar da burin kawo ci-gaba mai dogon zango.

“Yawancin abubuwan da majalisar ke ƙarawa ba a yi musu kyakkyawan tsari ba da lissafi ba, wanda hakan ke kawo naƙasu ga aiwatar da su ko cim ma manufarsu cikin nasara.

“Don haka muke ganin ya kamata majalisa ta rika yin taka tsantsan wajen amfani da wannan muhimmin iko nata. Ta sanya bukatar ƙasa da bunƙasa tattalin arziƙin a gaba tare da kawar da almubazzaranci da dukiyar al’umma.”