Wata kungiya a Jihar Kano ta aike wa majalisar dokokin jihar wasikar neman ta dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano, kuma ta rushe sabbin masarautun jihar.
Kungiyar mai suna ’Yan Dangwalen Jihar Kano, ta yi ikirarin cewa sauke Sanusi II daga sarauta ya kawo rabuwar kai da fargaba a tsakanin al’ummar Kano.
A ranar 3 ga watan Maris, 2020 ne tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ya tube rawanin Sarki Muhammadu Sanusi II, kan zargin rashin da’a da kin halartar tarukan aiki.
Gwamnatin Ganduje ta kuma yi kwaskwarima ga dokar masarautar jihar, inda ta kafa masarautu hudu — Bichi, Gaya, Rano, Gaya da Karaye — ta kuma nada musu sarakunan yanka. masu daraja ta daya.
- Yanzu-Yanzu: Mahara sun kashe sojoji 3 da ’yan banga 2 a Nasarawa
- An kashe kasurgumin dan bindiga a Abuja
A wasikarsu ga shugaban majalisar, mai dauke da sa hannun shugaban kuniyar Najib Abdulkdir Salati, ta ce, “Muna roko ka gabatar da wannan bukata ga gwamna sannan a fahimitar da ’yan majalisar jiha muhimmancin yin gyara ga dokar masarautu domin sauke sabbin sarakuna hudu da aka nada da kuma rushe masarautunsu.
“Mun san majalisa na da hurumi kan batun masarautu, don haka muke rokon ta da ta soke matakin da aka dauka a baya na sauke Sarki Sanusi II daga kujerarsa.
“Mun yi imanin cewa dawo da shi zai samar da hadin kai da zaman lafiya da aminci a Jihar Kano da makwabtanta, da kuma kawo cigaban jihar.”
Wakilinmu ya nemi karin bayani daga sakataren yada labaran majalisar dokokin jihar, Kamaludeen Sani Shawai, amma jami’in ya ce shi bai ga wasikar ba, amma ya yi alkawarin zai tuntubi wakilin namu daga bisani.