✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe kasurgumin dan bindiga a Abuja

An harbe Isa Dei-Dei har lahira ne a samamen da jami'an tsaro suka kai musu

’Yan sanda sun hallaka wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi yankin babban birnin tarayya, Abuja.

An kashe fitaccen dan bindigan mai suna Isa Dei-Dei ne ranar Litinin a yayin artabu da jami’an tsaro da suka  kai samame maboyar masu garkuwa da mutanen da suka addabi al’ummar yankin.

“Da suka hangi ’yan sandan sai suka fara guduwa, nan take jami’an suka bi su, lamarin da ya kai ga musayar wuta mai zafi, har aka kashe fitaccen dan bindiga Isa Dei-Dei,” in ji kakakin ’yan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi.

ACP Adejobi ya kuma sanar a safiyar yau Laraba cewa ragowar ’yan bindigar sun tsere da raunin harbin bindiga da suka samu a musayar wutar da jami’an tsaro.

Don haka ya roki jama’a musamman ma’aikatan lafiya da su sanar da jami’an tsaro idan suka ga wani da raunin harbin bindiga, domin a ci gaba da bincike.

Aminiya ta ruwaito yadda ’yan bindiga suka addabi yankunan da ke wajen garin Abuja, irin su Bwari, Kuje da sauransu, inda suke sace jama’a domin karbar kudin fansa, har su kashe wasu.