✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallah: An girke jami’an sibil difens 5,000 a Abuja

Hukumar ta bayar da tabbacin samar da tsaro a babban birnin tarayya, Abuja.

Hukumar Tsaron Sibil Difens (NSCDC), ta girke jami’anta 5,000 domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Babban Birnin Tarayya, Abuja a lokacin bukukuwan sallah ƙarama.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, CSC Samuel Idoko, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

A cewar sanarwar, Kwamandan NSCDC a Abuja, Olusola Odumosu, ya umarci jami’an hukumar da su tabbatar da tsaron kowane lungu da sako na Abuja.

“Mun tura rundunar jami’ai maza da mata ta musamman, don tabbatar da doka da oda, a Abuja” in ji Odumosu.

Odumosu, ya gargadi ɓata-gari da masu shirin tada zaune-tsaye da su kiyayi shiga hannun jami’an hukumar.

Ya buƙaci jami’an hukumar da su nuna ƙwarewa wajen aiwatar da aikinsu a lokacin da kuma bayan bukukuwan sallah.

“Rundunar za ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna Abuja da kuma kare muhimman kadarorin ƙasa a babban birnin tarayya, Abuja.

A cewarsa jami’an hukumar za su yi aiki ba dare ba rana domin bai wa birnin tsaro daga ɓata-gari.

Ya kuma bai wa mazauna birnin tabbacin haɗin gwiwa a tsakanin jami’an tsaro don yin aiki cikin ƙwarewa.

Kwamandan, ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmin Abuja murnar kammala azumin watan Ramadan tare da addu’ar Allah ya karɓi ibadunsu.