✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe sojoji 3 da ’yan banga 2 a Nasarawa

Wasu da ake zargin ’yan sa-kai ne a sun kashe sojoji uku da ’yan banga biyu a yankin Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.

Wasu da ake zargin ’yan sa-kai ne a sun kashe sojoji uku da ’yan banga biyu a yankin Umaisha  da ke Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.

Ana zargin ’yan sa-kan sun kai wa jami’an tsaron harin kwanton bauna ne a yankin Umaisha, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar.

Aminiya ta gano cewa wasu mahara sun kai hari a kwanan nan a kauyen Okudu inda suka kakkashe jama’a.

Kasa da mako guda kenan bayan a ranar 1 ga watan Fabrairu wasu mahara sun kashe mutane uku suka kona kadarori na miliyoyin kudi a kauyen.

An girke sojoji a kauyukan Katakpa da Okudu ne domin samar da zaman lafiya, sakamkon rikicin da aka samu tsakanin kauyukan biyu.