✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Za a dawo haska fim a sinima

Daga ranar Juma’a, 11 ga Satumba ce za a dawo haska fina-finai a sinimomi a fadin Najeriya bayan rufe su da aka yi sakamakon dokar…

Daga ranar Juma’a, 11 ga Satumba ce za a dawo haska fina-finai a sinimomi a fadin Najeriya bayan rufe su da aka yi sakamakon dokar kullen COVID-19.

Kungiyar Masu Lura da Sinimomi ta Kasa (CEAN) ce ta sanar da hakan, inda ta ce, “Mun dawo! Ku ziyarci duk wata sinimar da ke kusa da ku daga ranar 11 ga Satumba. Muna cikin murna wanda ba zai misaltu ba”.

A watan Maris ne kungiyar ’yan fim ta Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) ta umarci dukkannin kungiyoyi da shugabannin masana’antar fim da ke Arewa da su dakatar da gudanar da fina-finai saboda cutar COVID-19.

Umarnin, wanda a wancan lokacin ke dauke da sa hannun Sakataren Watsa Labaran kungiyar na kasa, Malam Al’amin Ciroma, ya nuna cewa an dauki matakin ne domin kiyaye yaduwar cutar.

A farkon wannan watan ne kuma aka shiga mataki na uku cikin matakai uku na cire dokar kullen wadda aka sanya domin kiyaye yaduwar cutar Covid-19.

A mataki na ukun, Gwanatin Tarayya ta ba da damar a ci gaba da harkokin nishadi, ciki har da bude sinimomi da sauransu.

Rufe sinimomi ya sanya da dama daga cikin masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood sun juya akalarsu zuwa manhajar YouTube, inda suke shirya fina-finai masu dogon zango, da wakoki.

Domin murnar wannan umarni, Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa sanarwar a shafinsa na Instagram, inda ya ce, “Alhamdulillah”.