✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kannywood ta ba wa Hisbah tabbacin goyon baya a Kano

Bayan ce-ce-ku-ce, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sake zama da daraktoci da furdusoshi da jarumai da sauran ’yan Kannywood kuma sun ba ta tabbacin…

Bayan ce-ce-ku-ce, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sake zama da daraktoci da furdusoshi da jarumai da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood don tsaftace harkar fim da nufin kau da ayyukan badala a jihar.

A jawabansu daban-daban, Shugaban Kungiyar MOPPAN ta Kasa Dokta Ahmad Sarari da takwaransa na Jihar Kano Ado Ahmad Gidan Dabino da Shugaban Kungiyar Jarumai Alasan Kwalle sun nuna jin dadinsu game da taron inda suka sha alwashin ba wa Hisbah goyon baya tare da alkawarin cewa nan gaba za a samu gyara a harkar fim din.

Wannan shi ya kawo karshen ce-ce ku-cen da aka yi ta yi game da ganawar Hukumar da ’yan fim na farko, wanda mafi yawansu suka kaurace wa bisa hujjar cewa Hisbar ba ta bi hanyar da ta dace wajen gayyatar su ba.

Hukumar ta sake mika musu goron gayyata a karo na biyu wanda suka amsa a karkashin jagorancin dan gidansu wato Shugaban Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano Abba Almustapha.

Kwamanda-Janar na Hukumar Hisbah Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa korafe-korafe da suke yawan samu daga Kanawa da sauran sassan Najeriya kan yadda ’yan fim ke nuna abubuwan da suka saba wa addinin Musulunci da al’adun Hausawa a cikin finafinansu ya sa suka ga dacewar zama da masu ruwa da tsaki a harkar fim don lalubo hanyoyin kawo gyara a cikin harkar.

“Ita Hukumar Hisbah an kafa ta ne don ta saita al’umma a kan koyarwar addinin tare da yi musu katanga daga aikata munanan ayyuka.

“Muna so a lalubo hanyoyin da za a rage nuna abubuwa da suke na tir tare da ci gaba da nuna abubuwa da za su dabbaka addinin da kyawawan koyarwar al’adun Hausawa a harkar fim,” in ji Daurawa.

A nasa bangaren, Abba Almustapha ya bayyana cewa tuni ’yan fim din suka amince za su zama masu bin doka.

Abba Almustapha ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba hukumomin biyu za su shirya taron kara wa juna sani da ’yayan Kannywood don ilimintar da su kan abin da ya shafi fim ta fuskar addinin Musulunci inda za a gayyato fitattun malaman Musulunci don tattauna tare da lalubo hanyoyin da za a kai harkar fim din ga tudun mun tsira.