✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kannywood: Mahaifiyar Haruna Talle Maifata ta rasu

Za a yi jana'izarta a unguwar Mil Tara da ke Jihar Kano.

Allah Ya yi wa mahaifiyar jarumin fina-finan Kannywood, Haruna Talle Maifata rasuwa.

Jarumin ya wallafa sanarwar rasuwar mahaifiyar tasa a shafinsa na Instagram, a daren ranar Laraba, bayan ta yi gajeriyar rashin lafiya.

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah Ya yi wa mahaifiyata rasuwa yau, za a yi jana’izarta a kofar gidanta da ke Kano Mil Tara,” kamar yadda ya wallafa.

Tuni jaruman Kannywood da sauran taurari kamar su Abba El-Mustapha, Madam Korede, Nazifi Asnanic, Hassan Giggis, Garzali Miko da sauransu suka fara yi masa masa ta’aziyya game da rashin mahaifiyar tasa.

A baya-bayan nan masana’antar ta sha fama da mutuwar jarumanta, kamar su Ahmed Aliyu Tage, Sani SK da sauransu.