Mazauna wasu unguwanni a Jihar Kano sun koka kan yadda a makonnin baya-bayan ake fama da matsalar karancin wutar lantarki.
Wasu mazauna unguwar Rijiyar Zaki da ke Karamar Hukumar Ungogo a Jihar da Aminiya ta tattauna da su, sun bayyana halin kunci da rashin wutar lantarkin ya jefa su a ciki na tsawon kwanaki.
- Za a shafe kwana 3 ana ruwan sama da tsawa a Jihohin Arewa
- Karya Darajar Naira: Ɗangote ya faɗo daga mai kuɗin Afirka
A cewar wani tela dan asalin Jihar Kogi mazaunin unguwar, Yakubu Akaba, ya ce “a gaskiya abin da ’yan NEPA ke yi a mana a ’yan kwanakin nan ba sa kyautawa.
“Mun shafe fiye da kwanaki hudu babu wuta kuma ga shi sai da ita kekunan mu da dinki ke amfani.
“Inda Allah ya taimake ni ma wasu lokutan idan babu wutar nakan yi amfani da keke dinki na gargagiya wanda ba ya amfani da wutar lantarki.
“Don a wannan zamanin da man fetur ya yi tsada ba zan yi jimirin kunna jannareta ba domin kuwa babu wata riba da mutum zai tsira da ita don ko su kayayyakin dinkin sun yi tsada a kasuwa.
“Da me za mu ji. Allah dai Ya kyauta Ya kawo mana saukin wannan lamari,” a cewar Akaba.
Haka kuma wani saurayi da ya kammala karatun digiri kuma yake sanaar POS gabanin tafiya bautar kasa, Yusuf Bala Usmann, ya ce gaskiya muna jin jiki saboda wannan matsala ta rashin wutar lantarki.
Ya shaida wa Aminiya cewa, “duk da cewa sana’ar da nake yi ba ta bukatar wutar lantarki sosai, amma naurar POS da kuma wayar salula da nake amfani da su wajen tafiyar da wannan sanaa a wasu lokutan caji yakan yanke musu.
“Don ko rannan haka ina ji ina gani da wani ya zo cirar kudi amma saboda rashin caji a na’urar POS dole na hakura.
Shi ma wani mai sana’ar sayar da ruwa da lemuka, Baba Madaki, ya ce “ai kwana na biyu ke nan ko shago ban bude ba, saboda ko kankarar da nake saye na zuba wa ruwa da lemo a yanzu idan mun je saye sai a ce ai babu saboda rashin wutar lantarki.
“Sai dai akwai wani mai sayar da kankara mai suna Jaafar da muka je neman kankara wurinsa, ya ce zai kunna jannaretansa ya kwana saboda idan mun zo saye mu samu.
“Ya ce mana ba ya jin dadi kullum mu zo saye amma a tarar babu kankarar kuma da yawan masu saye sana’a’o’insu sun dogara ne kan kankarar musamman a wannan lokaci da ake kwala rana da tsananin zafi.
“Sai dai wani abu mamaki shi ne yadda mai sayar da kankarar ya ce ba zai kara mana farashi ba, gaskiya na ji dadi don kuwa irin wadannan mutane ake so masu jin tausayin jama’a musamman a lokacin da aka shiga tsanani,” in ji Madaki.
Bayanai na nuna cewa, daga jiya Lahadi zuwa yau Litinin, an samu wutar lantarki a unguwar ta Rijiyar Zaki, wadda ta sanya mazauna suka shiga bayyana farin cikinsu da wannan lamari.
“Eh, gaskiya daga jiya Lahadi zuwa yau Litinin mun samu wuta, don yanzu ko kayan da ke cikin firinji na sun kankare laakari da cewa an kwana da wuta.
“A yanzu ko kai da na san kana yawan zuwa sayen Coca Cola duk wacce kake so, ta kwalba ko ta roba za ka same ta a rabe kamar wadda jaura ta wuce ta kanta,” a cewar wani mai kanti mai suna Rabi’u Nagarta.
Dalilin rashin wutar lantarki a Kano —KEDCO
A wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya fitar a ranar Lahadi, ya alakanta rashin wutar da matsalar da aka samu tun daga Kamfanin Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (TCN) layin Shiroro zuwa Kaduna mai nauyin 330KV a ma’aunin karfin lantarki.
A sanarwar da babban jami’in sadarwa na KEDCO, Sani Bala Sani ya fitar, ya bai wa abokan huldarsu na jihohin Kano da Katsina da Jigawa hakuri dangane da wannan yanayi da aka tsinci kai.
A cikin sanarwar, ya ce matsalar ta auku ne tun bayan lalacewar da manyan layukan samar da wutarsu guda biyu suka yi a ranar 26 ga watan Afrilu da kuma ranar 11 ga watan Yunin wannan shekara.
Sai dai ya ce daga jiya Lahadi an kammala gyare-gyaren kuma komai ya daidaita za a ci gaba da samun wutar lantarkin yadda ya kamata.
Ya nanata bai wa abokan huldarsu hakuri kan duk wani matsinda lamarin ya jefa su a ciki a kwanakin nan.
Tarihin Wutar Lantarki a Najeriya
Samun tsayayyar wutar lantarki shi ne kashin bayan ci gaban tattalin arzukin kowace kasa, akasin hakan kuwa shi ke kawo tafiyar hawainiyar tattalin arzikinta.
Tun a shekarar 1896 ne aka fara kawo wutar lantarki a Najeriya, wato shekaru 15 bayan da aka fara samar da wutar lantarkin a Ingila.
A wancan lokacin ana amfani da injinnan janareta mai karfin kilowatz 60 kawai a Najeriya.
A shekarar 1946 gwamnatin mulkin mallaka a Najeriya ta kafa hukumar sa ido kan samar da wutar lantarki a jahar Lagas.
Kuma a shekarar 1950 ne aka kafa hukumar samarda wutar lantarki ga kasar baki daya wato Electricity Corporation of Nageria ECN, wannan ya nuna kenan shekaru da dama kafin Najeriya ta samu ‘yancin kanta a shekaru 50 din da suka wuce, kasar ke amfani da wutar lantarki, ko da yake yawan wadda ake amfani da ita ya zuwa wancan lokacin bata kama kafar wadda ake bukata shekaru bayan samun ‘yancin kai ba.
Tun daga shekarun 1970 Najeriya ta fara samar wa makwabciyarta kasar Nijar wutar lantarki.
An kafa hukumar samar da wutar lantarki ta kasa wato NEPA a shekarar 1972 domin sa ido kan yadda ake rarraba wutar lantarki a duk fadin kasar, da kuma kudaden da ake samarwa ta hanyar wutar lantarkin.
Kuma tun bayan da aka kafa hukumar shekaru sama da talatin din da suka wuce mahukuntan kasar ke cewa suna aiki kan yadda za’a samar da isashiyar wutar lantarki a duk fadin kasar, yayin da bukatar wutar ke karuwa, a kasar da a yanzu haka al’ummarta ta haura miliyan 140.
Sai dai kuma duk da arzikin makamashi da albarkatun kasar da Najeriya ke da su, a madadin a samu ci gaba sai dai a kullum kara cibaya ake, inda kawo wannan lokaci yawancin ‘yan Najeriya basa samun wutar lantarkin, kuma wadanda ke samun ma ba ko yaushe ne ake basu wutar ba.