Kungiyar Shugabannin Kamfanonin Jiragen Sama ta Najeriya ta bayyana damuwa kan karancin man jirgin da ke ke kara ta’azzara a kasar nan, wanda ke haddasa dagewa ko ma soke tafiye-tafiyen baki daya.
Kan haka ne kungiyar ta bakin kakakinta, Farfesa Obiora Okonkwo ta ce suna aiki kafada-kafada da masu siyar da man da Gwamnatin Tarayya da ma sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin an samu man kuma a farashin mai rahusa.
- EFCC ta kama Akanta-Janar, Ahmed Idris kan zargin almundahanar N80bn
- Hukumar ’Yan sandan Najeriya ta yi wa Magu karin girma
“Muna sanar da al’umma cewa za a dinga samun soke tashin jirgi daga ’ya’yan kungiyarmu, amma ba a son ranmu ba ne, rashin mai ne ya janyo hakan,” in ji shi
A karshe kakakin Kungiyar shugabannin kamfanonin jirgen saman ya gode wa al’ummar Najeriya bisa nuna fahimtarsu kan halin da ake ciki kamar ko yaushe, hadi da alkawarin kungiyar za ta dauki duk matakan da suka kamata domin dawo da zirga-zirgar jiragen sama ba tare da wannan matsala ba kamar yada yake a baya.